You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848689

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

Solskjaer ya caccaki halayyar 'yan wasan Man United

Ole Gunnar Solskjaer Ole Gunnar Solskjaer

Ole Gunnar Solskjaer ya caccaki halayyar 'yan wasan Manchester United a lokacin da ya horar da ƙungiyar, a cewarsa ƙwazonsu bai kai yadda ake zato ba.

United ta kori Solskjaer a watan Nuwamban 2021, bayan kusan shekara uku yana jan ragamar ƙungiyar.

Erik ten Hag, wanda ya maye gurbin Solskjaer ya ce 'yan wasan United ba su da kyakkyawar dabi'a lokacin da ya je Old Trafford a Mayun 2022.

''Wasu 'yan wasan ba su da ƙwarewar da ta kamata har ake ganin gogaggu ne'' in ji Solskjaer mai shekara 50.

Tsohon ɗan wasan United da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Norway ya ƙara da cewar ''Ba zan kama suna ba, amma na yi matuƙar baƙin ciki da wasu suka ƙi karɓar muƙamin kyaftin.''

''Na ji ɓacin rai lokacin da wasu 'yan wasan suka ce ba za su yi atisaye ko buga wasa ba, don kawai sai sun bar ƙungiyar kamar yadda suka tsara.''

United ta zo ta biyu a gasar Premier League a kakar 2020/21, sannan aka doke ta a wasan ƙarshe a bugun fenariti a hannun Villareal yayin karawar gasar Europa League.

Solskjaer ne ya sayo Jadon Sancho da Raphael Varane da dawo da Christiano Ronaldo.

Sai dai an kore shi bayan jan ragamar wasa 12 da fara Premier League, sakamakon da Watford ta doke United 4-1.

Solskjaer ya sanar cewar United ta kasa sayen 'yan ƙwallon da ya nema kulob ɗin ya ɗauko.

Ciki har da Erling Haaland, wanda ya koma RB Salzburg a 2019 da Declan Rice da kuma Jude Bellingham.

Ya ƙara da cewar ya daɗe yana fatan United ta ɗauki Harry Kane, wanda yanzu ya koma Bayern Munich da taka leda.