You are here: HomeAfricaBBC2021 05 01Article 1248520

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Solskjaer bai taba haura daf da karshe a karawa hudu ba

Ole Gunnar Solskjaer, Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, Kocin Manchester United

Manchester United za ta karbi bakuncin Roma a wasan farko na daf da karshe a Europa League da za su kara ranar Alhamis a Old Trafford.

Sau hudu kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya kai kungiyar wasannin daf da karshe a karawa daban-daban, amma baya haura matakin.

United karkashin Solskjaer tana samun ci gaba a wasannin Premier League, wadda take ta biyu a kakar bana, bayan da ta kare ta shida da ta uku a shekaru biyu baya.

Sai dai kungiyar ta dade ba ta lashe kowanne irin kofi ba, wanda wannan babban kalubale ne a gaban United daya daga fitattun kungiyoyin tamaula a duniya.

Rabon da United ta lashe kofi tun bayan Europa League da ta dauka a 2017 da Jose Mourinho ya yi mata wannan bajintar.

Cikin wasannin da United ta kasa haura daf da karshe sun hada da rashin nasara a hannun Manchester City karo biyu a League Cup da wasan daf da karshe da Chelsea a FA Cup a bara.

Haka kuma ta yi rashin nasara a hannun Sevilla a gasar Europa League duk karkashin kocin United, Solskjaer.

Yin nasarar da United ta yi a kan Granada a quarter finals a bana, zai bai wa Solskjaer kwarin giwar kai wa wasan karshe a Europa League na bana.

Tun farkon shiga shekarar nan Roma tana ta hudu a kan teburin Serie A hankalinta kwance, sai ta ci karo da koma baya, inda ta ci wasa daya daga bakwai da hakan ya sa ta koma ta bakwai a gasar ta Italiya.

Wannan sakamakon ya sa matsi ga kocin Roma, Paulo Fonseca wanda yake hangen lashe Europa League na bana zai sa ya samu kwanciyar hankali a kungiyar.