You are here: HomeAfricaBBC2023 01 17Article 1697003

BBC Hausa of Tuesday, 17 January 2023

Source: BBC

'Shugaba Putin na amfani da abinci a matsayin makami'

Shugaban Rasha, Vladimir Putin Shugaban Rasha, Vladimir Putin

Shugaban daya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa taki a duniya ya zargi Shugaban Rasha, Vladmir Putin da amfani da abinci a matsayin makami.

Da yake magana da BBC, a farkon taron tattalin arziki na Duniya a Davos, shugaban Kamfanin Yara International, Svein Tore Holsether, ya ce dogaron da duniya ta yi kan takin Rasha ya sa ya zama wani makami mai karfin gaske.


Rasha babbar mai samar da taki ce da sinadarin ammonia - wani abu mai muhimmanci wajen samar da taki mai yawa.

Sai dai tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine, an takaita yawan takin da kasar ke samarwa.

Yakin ya kuma janyo hauhawar farashin iskar gas da ke da matukar muhimmanci wajen samar da takin.Shugaban kamfanin ya kuma bukaci kasashe su rage yawan dogaron da suke kan Rasha.

Yanzu haka ana zargin Putin da amfani da makamashi a matsayin makamin yaki, inda dakarunsa ke kai hare hare tashoshin da ke samar da wutar lantarki a Ukraine.