You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853963

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa

Joe Biden, shugaban Amurka Joe Biden, shugaban Amurka

Ƴan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Republican sun bayyana ranarsu ta farko ta kaddamar da bincike kan Shugaban ƙasar Joe Biden a matsayin nasara.

Sai dai biyu daga cikin ƙwararrunsu masu bayar da sheda sun ce zuwa yanzu babu isasshiyar shedar da za ta tallafa wajen tsigewar.

Harkokin kasuwanci na ɗan shugaban ƙasar Hunter su ne suka mamaye zaman da majalisar ta yi a ranar Alhamis na tattauna batun shirin tsigewar.

Ƴan majalisar na jam'iyyar Republican sun yi zargin cewa Shugaba Biden ya amfana da harkokin kasuwancin dan nasa.

Fadar shugaban ƙasar, White House ta bayyana binciken a matsayin wani abu na neman son-a-sani na siyasa.

Ƴan majalisar na Republican sun yi shekaru suna gudanar da bincike a kan ɗan shugaban kamar yadda ma'aikatar shari'a ta Amurka ita ma take yi.

Sai dai babu ɗaya daga cikinsu da ya samu shedar da ke nuna cewa Joe Biden walau a matsayinsa na shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa ya saba wa ƙa'idojin aikinsa ko kuma ya karɓi cin hanci.

Duka wannan na kasancewa ne yayin da shi ma Shugaba Biden ya caccaki tsohon shugaban ƙasar Donald Trump inda ya bayyana shi a matsayin barazana ga dumukuraɗiyyar Amurka.

Biden ya ce ƙoƙarin Trump na neman sake samun shugabancin ƙasar na cike ne tattare ne da neman ramuwar gayya

Mista Biden ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar wajen taron tunawa da marigayin dan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican, John McCain, a Arizona.

Ya ce jam'iyyar Republican duk da cewa ba dukkanin mabiyanta ba ne ke bin aƙidar Trump ɗin to amma a yanzu masu tsattsauran ra'ayi ne ke tafiyar da ita.

Shugaban ya zargi Trump da magoya bayansa da yada aƙidoji na ƙarya da neman haddasa husuma.

Duk da cewa sai nan da shekara ɗaya da ƴan watanni za a yi zaɓen shugaban ƙasar na gaba to amma sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ya nuna za a yi kusan kan-kan-kan idan Trump ya samu tikitin yi wa Republican takara.