You are here: HomeAfricaBBC2021 05 01Article 1248532

BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Shin don gwagware aka ƙirƙiri al'adar Tashe a lokacin Azumi?

Tashe wata al'adar al'ummar Hausawa ce da ake yi a cikin watan azumin Ramadan Tashe wata al'adar al'ummar Hausawa ce da ake yi a cikin watan azumin Ramadan

Tashe wata al'adar al'ummar Hausawa ce da ake yi a cikin watan azumin Ramadan.

Kuma tashe, wasanni ne na gargajiya da yara maza da mata ke gudanarwa domin nishaɗi da kuma samun sadaka bayan kwana 10 na azumin watan Ramadan.

Malam Yusuf Muhammad na sashen Harsuna Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano ya yi wa BBC bayani kan tarihin Tashe da muhimmancinsa da kuma tasirin zamani.

Asalin kalmar Tashe

Masanin ya ce kalmar 'tashe' ta samo asali ne daga kalmar 'tashi' wato mutum ya tashi domin sahur yayin daukar azumi.

Wasannin tashe sun samo asali ne daga Nalako, wanda sarki ne yake naɗa shi a matsayin sarkin gwagware - wadanda suka daɗe ba su yi aure ba.

Nalako yana kewayawa ne yana wasanni don tashin gwagware daga bacci saboda ba su da matan da za su riƙa tashinsu.

Kuma da daddare ne Nalako yake wasa bayan an gama sahur, daga nan ne mutane suka fara kwaikwayonsa suna yin tashe.

Kuma Malam Yusuf ya ce ana smaun nishaɗi a Tashe bayan an sha wahalar azumi. "Saboda gaurantaka aka naɗa shi sarkin gwagware."

Asalin kalmar tashe shi ne gwagware su tashi su yi sahur tun da ba su da wanda zai tayar da su.

Wannan al'ada ce bayan zuwan addini musulunci ƙasar Hausa, don haka galibi irin waken da ake yi ana shigar da abin da ya danganci addini, musamman kalmomi da ke nuna Bahaushe addininsa musulunci ne.

Rabe-raben Tashe

Akwai rukuni na masu aiwatar da Tashe - akwai na yara maza da mata.

Tashen maza akwai wasan yara maza na nuna jarumta misali wasan tashen 'inda hali ya yi ba gudu ba tsoro" yara na sanya kayayyaki na al'ada kamar guru da laya da wuƙa da takobi na katako suna zagaya wa cikin gari suna nishaɗantar da magidanta, suna cewa:

"Idan za a ba mu a ba mu, Aljanna sai mun zaɓa

kai yaro ɗaga cikinka ka yanka, Idan ba maza ba tsoro"

Akwai kuma tashen "Jatau mai magani" da ke nuna maganin gargajiya na Bahaushe.

A bangaren mata, akwai wasan "Mairama da Daudu inda 'yan mata sukan yi shiga ta namiji a shimfiɗa tabarwa ana rera baituka kamar

"Dauko ruwansa ki ba shi

Dauko tuwonsa ki ba shi

Dauko furarsa ki ba shi

Sai kin durƙusa ki ba shi, sai kin rausaya ki ba shi"

Malam Yusuf ya ce wannan irin tashen na mata yana nuna wa matan Hausawa irin zaman da ya kamata su yi na biyayya a gidan miji da kuma kyautata wa miji.

Akwai kuma maganar kwalliya da nishaɗar da miji don kada ya fita ya kula wasu.

Wa ake yi wa tashe

Lokacin Tashe ana shiga gidaje ne inda yara suke shiga gida-gida suna aiwatar da wasanninsu na tashe. Wani lokaci ana tashe da rana amma an fi yi bayan sallar isha'i.

Ana yi wa kuma sarakuna tashe, amma Malam Yusuf ya ce sarkin gwagware Nalako yake yi wa sarakuna tashe.

Ya kuma ce akwai wasu masarautun da ke ba yara damar yin tashe a kofar maigari, inda yara za su taru su yi wasanninsu na tashe a gaban maigari.

Muhimmacin tashe

Tashe yana taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihin Hausawa kamar yadda masana al'adun Hausawa suka bayyana.

Masana na ganin ba don wasannin tashe ba, da abubuwa da dama yanzu an manta da su.

Rukunin kayayyakin makamai da tufafin Hausawa kamar zannuwa da riguna na dauri duk ana nunawa a tashe kuma yanzu mata da maza na yanzu ba su san irin kayayyakin ba.

Tashe kuma yana fito da al'ada ta magungunan gargajiya, kuma yanzu da yawa yara ba su san ire-iren abubuwan da za su sha ba a gargajiyance kamar idan ciki na ciwo a dauko kanwa a sha.

Akwai kuma gyaran zamantakewar al'adar Bahaushe musamman a ɓangaren aure ga mata. Yawan rigingimu musamman a auren farko da rashin daraja miji da ake samu a yanzu, ana iya alaƙanta shi a wannan zamanin da rashin gudanar da wasannin tashe.

Tasirin Zamani

Masanin ya ce zamani ya fara yin tasiri ga al'adar Bahaushe ta tashe kuma a dukkanin ɓangarorin da ke gudanar da al'adar.

Zamani ya kawo waɗansu abubuwa da dama kamar na siyasa inda yara suke kwaikwayon ɗan siyasa da irin shigarsa. Malam Yusuf ya ce duk wannan zamani ne ya kawo shi domin can baya babu hakarar majalisa.

Akwai kuma wasan ƴan mata da maza ke kwaikwayo inda wani namiji zai saka ƙananan kayan mata da rigar mama, ya yi kama da mace, sai a riƙa cewa - ƴar makarantar boko ta yi ciki an koro ta.

Wannan tasiri ne na zamani domin lokacin da aka fara tashe babu makarantun Boko.