You are here: HomeAfricaBBC2023 09 01Article 1836335

BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Shin Ecowas ta fara ba da kai ga sojojin Nijar ne?

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Ana ci gaba da tsokaci, tun bayan da shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Tinubu ya ba da shawara ga sabbin shugabannin mulkin sojan Nijar, su mayar da mulki hannun farar hula a cikin wata tara.

Kalaman su ne karon farko da wani jami'in Ecowas ya fito bainar jama'a yana tattauna batun wani shirin miƙa mulki ga shugabannin sojin Nijar.

Ecowas dai ta ƙaƙaba jerin takunkumai ga Nijar, bayan hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli, sannan ta yi barazanar auka wa Nijar da ƙarfin soja, matuƙar ba su mayar da Bazoum kan karagar mulki ba.

Sabbin shugabannin mulkin sojin Nijar dai sun fitar da matsayinsu, inda suka ce suna son kafa wani shirin gwamnatin riƙon ƙwarya da ba zai wuce shekara uku ba kafin mayar da ƙasar kan tsarin mulki.

Sai dai, a baya-bayan nan al'amura sun daɗa rincaɓewa, bayan sun umarci 'yan sandan ƙasar su kori jakadan Faransa daga Nijar, yayin da zaman ɗar-ɗar ke ƙaruwa da babbar abokiyar ƙawance a yaƙin da Nijar ɗin ke yi da masu iƙirarin jihadi.

Tinubu dai ya ce Najeriya ta koma kan tsarin mulkin dimokraɗiyya a shekarar 1999 bayan wani shirin miƙa mulki na tsawon wata tara, a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda a yanzu yake jagorantar jami'an diflomasiyyar Ecowas da ke ganawa da sojojin Nijar.

Wata sanarwa ta ambato cewa "shugaban ƙasar yana ganin babu wani dalili da zai hana a kwatanta haka a Nijar, matuƙar shugabannin mulkin sojan ƙasar da gaske suke yi".

Aljeriya, muhimmiyar maƙwabciyar Nijar ta arewa, ta gana da shugabannin Afirka ta Yamma a yunƙurinta na ganin an kauce wa amfani da ƙarfin soja a kan Nijar, har ma ta gabatar da wani ƙudurin miƙa mulki hannun farar hula a cikin wata shida.

Sai dai sanarwar Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ta ce Ecowas ba za ta sassauta takunkuman da ta sanya wa Nijar ba, har sai sojoji masu mulki sun aiwatar da "ƙwararan sauye-sauye".

"Matakin da sojojin suka ɗauka ba za a yarda shi ba. Idan sun aiwatar da sauye-sauye cikin gaggawa, mu ma cikin sauri za mu ɗaga ƙafa a takunkuman da aka sanya don rage wahalhalun rayuwa da muke gani a Nijar," a cewar sanarwar.

Kifar da gwamnati a Nijar, ya haddasa damuwa a faɗin Afirka ta Yamma, inda tun shekara ta 2020, sojoji suka ƙwace mulki a ƙasashen Mali da Guinea da kuma Burkina Faso.

Fargaba a kan bazuwar juyin mulki ta ƙara tsanani saboda boren da sojoji suka yi cikin wannan mako a Gabon, inda suka hamɓarar da Shugaba Ali Bongo, jim kaɗan da ayyana shi matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ƙarshen makon jiya da ake matuƙar taƙaddama kansa.

Rikicin diflomasiyya

Sabuwar gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta kuma shiga rikicin siyasa da gwamnatin Paris, har ma tuɓe wa jakadan Faransa rigar kariyar diflomasiyya kuma ta umarci 'yan sanda su kore shi daga ƙasar.

AFP ya ce wata wasiƙa da ya gani ranar Alhamis ta ce jakadan na Faransa "a yanzu ba shi da wata alfarma da rigar kariyar da ake bai wa masu riƙe da matsayin jami'an diflomasiyya na ofishin jakadancin Faransa".

Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa ta yi tsami bayan juyin mulkin watan Yuli lokacin da gwamnatin birnin Paris ta tsaya kai da fata tana goyon bayan Bazoum, kuma ta ƙi martaba sabbin masu mulkin na Nijar.

A ranar Juma'ar makon jiya ne, hukumomi suka bai wa jakadan Faransa, Sylvain Itte sa'a 48 ya fice daga Nijar. Sai dai, Faransa ta ƙi amincewa da buƙatar, tana cewa gwamnatin ba ta da hurumi a shari'ance ta ba da irin wannan umarni.

Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa, Kanal Pierre Gaudilliere, kamar yadda AFP ya ambato ya yi gargaɗi a ranar Alhamis cewa "dakarun Faransa a shirye suke su mayar da martani a kan duk wata rikita-rikita a zaman ɗar-ɗar ɗin da ake yi matuƙar zai iya cutar da harkokin diflomasiyya da na sojin Faransa a Nijar".

Faransa na da dakarun soji kimanin 1,500 a Nijar, da yawansu na jibge a wani sansanin sojojin sama da ke kusa da babban birnin, kuma an tura su ƙasar ne don su taimaka wajen yaƙi da wani rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi a Nijar.

A ranar 3 ga watan Agusta ne, sojoji masu mulki a Nijar suka soke yarjejeniyoyin soji da Faransa, matakin da gwamnati a birnin Paris shi ma ta yi biris da shi bisa hujjar rashin halarci.

Wata ƙungiya da aka kafa bayan juyin mulkin mai suna Garkuwar 'Yan Kishin Ƙasa wajen Kare Iyakokin Nijar (FPS) ta jagoranci gabatar da buƙatun jama'a masu kira ga shugabannin juyin mulkin su ɗauki tsattsauran mataki.

Tana dai kira ne a gudanar da wani "gawurtaccen" maci ranar Asabar a sansanin sojojin Faransa, daga nan kuma a yi zaman dirshen har sai sojojin sun bar ƙasar.

Tura dakaru

Ƙasar Nijar dai wadda Faransa ta taɓa yi wa mulkin mallaka a tsakiyar yankin Sahel, tana fama da rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya guda biyu -- wani da ya kwaranya zuwa kudu maso gabashin Nijar daga rikicin tsawon shekaru a Najeriya mai maƙwabtaka da kuma wani rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya da ke tsallaka wa kudu maso yammacin Nijar daga Mali da Burkina Faso.

Bazoum ya hau mulki ne a shekara ta 2021 bayan zaɓen dimokraɗiyya -- wani muhimmin abin tarihi a ƙasar wadda ba ta taɓa ganin miƙa mulki zuwa wata sabuwar gwamnati cikin kwanciyar hankali ba tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960.

AFP ya ce sau biyu, Bazoum yana fuskantar yunƙurin juyin mulki kafin dakarun tsaron fadar gwamnatinsa su yi nasarar hamɓarar da shi a watan Yuli.

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) ta mayar da martani ta hanyar yin gargaɗin cewa za ta iya amfani da ƙarfin soja wajen mayar da mulkin dimokraɗiyya idan ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin ta diflomasiyya ya ci tura.

Cikin hanzari don nuna goyon baya ga abokan ƙawancensu na Nijar, ƙasashen Mali da Burkina Faso sun ce duk wani mataki irin wancan za su ɗauke shi a matsayin "shelar ƙaddamar da yaƙi" a kansu.

Burkina Faso ta amince da wani daftarin doka da ke ba da izinin tura dakarun sojoji zuwa Nijar, a cewar wata sanarwar gwamnati a Ouagadougou ranar Alhamis.