You are here: HomeAfricaBBC2021 05 03Article 1249384

BBC Hausa of Monday, 3 May 2021

Source: BBC

Shekara tara kenan da Real Madrid ta ci La Liga na 32

Real Madrid ayayin da suka yi nasara a La Ligan shekara 2012 Real Madrid ayayin da suka yi nasara a La Ligan shekara 2012

Ranar 2 ga watan Mayun 2012, Real Madrid ta doke Athletic 3-0 a St Mames ta lashe kofin gasar La Liga kuma na 32 jumulla.

Real din ta yi nasarar cin kofin kasar Spaniya a lokacin da ya rage saura karawa biyu a karkare wasannin La Liga a lokacin.

Wadan da suka ci mata kwallayen sun hada Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da kuma Cristiano Ronaldo.

A kakar ce Madrid ta hada maki 100 da cin kwallo 121, kuma Cristiano Ronaldo ne ya zama kan gaba a zura kwallaye a raga mai 46.

A kuma kakar ce Real Madrid ta yi bikin cika shekara 110 da kafuwa a kakar ta 2011/12.

Kungiyar ita ce ta farko da ta hada maki 100 a tarihi da cin kwallo 121 a gasar ta La Liga.

Haka kuma kungiyar ta yi bajintar lashe wasa 32 da yin nasara a karawa 16 a waje.

Real wadda ta lashe La Liga a kakar 2011/12 ta bai wa Barcelona tazarar maki tara tsakani wadda ta yi ta biyu.

Jose Mourinho ne ya ja ragamar 'yan wasa da ta kai Real ta ci La Liga a kakar, hakan ya sa kocin ya lashe kofin kasar Portugal da Ingila da Italiya da kuma Spaniya.

Real Madrid mai kofin La Liga 34 jumulla kawo yanzu ta kara lashe biyu a kakar 2016/17 da kuma 2019/20,