You are here: HomeAfricaBBC2021 05 25Article 1269856

BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Shekara daya bayan kisan George Floyd: Samun Derek Chauvin da laifi 'ba wani abun murna ba ne'

Kisan George Floyd ya jawo zanga zanga a fadin duniya Kisan George Floyd ya jawo zanga zanga a fadin duniya

Bidiyonda ya karade shafukan intanet da ke nuna halin da George Floyd ya shiga ciki a kafin karshen rayuwarsa ranar 25 ga watan Mayu na 2020, ya jawo tarzoma a fadin duniya da kuma batun wariyar launin fata da ma musgunawar da 'yan sanda suke yi wa bakaen fata.

Wasu na gaanin matakin ba kasafai ba da aka dauka na kama dan sandan Amurka farar fata Derek Chauvin da laifin kisan bakar fata ya nuna cewa fannin shari'ar kasar yana aiki.

Sai dai wasu na ganin hakan ba komai ba ne.

Toni, wani matasi dan shekara 28 da ke aikin daukar hoto, ya ji batun yanke hukuncin lokacin da yake cikin dakin otal din da ya zauna bayan ya dawo daga wurin daukar hoto.

"Ba zan iya bayyana yanayin da na shiga ba, amma tabbas ba wai yanayi ne na murna ba," in ji shi. "Abin arashi shi ne na ji kamar an dauke min wani babban nauyi, na ja dogon numfashi.

"Shi hakan ya sa na samun kwarin gwiwa kan fannin shari'a? Ba haka ba ne."

A lokacin da yake dab da mutuwa, George Floyd ya yi kuka fiye da sau 20, yana cewa ba ya iya yin numfashi sakamakon danne wuyansa da dan sandan ya yi da gwiwarsa a kan titin birnin Minneapolis.

A watan Afrilu, wani alkali ya samu Chauvin da laifin kisan kai bayan an kwashe mako uku ana shari'a.

Ana sa ran zartar masa da hukuncin ranar 16 ga watan Yuni.

A shekarar 2020, na tattauna da wasu matasa uku bakaken fata daga bangarori daban-daban na duniya game da kisan George Floyd.

Shekara daya bayan haka, na gana da Toni Adepegba, Laëtitia Kandolo da kuma Nia Dumas domin na ji ra'ayinsu game da abin da samun dan sandan da laifi yaker nufi a gare su, da kuma, kamar ni, sun yi fama kafin su bayyana yadda suka ji game da hukuncin.

'Babu abin murna'

Duk da murnar da aka yi maras yawa, ba a jima ba na fahimci irin halin bakin ciki da kuncin da mutane suke ciki. Kuma ba ni kadai ba ne na fahimci hakan.

"Ina gida kuma na ga [lokacin da aka sanar da hukuncin] inda na duba Instagram da Twitter domin na samu karin bayani," a cewar Laëtitia.

"Ina ganin ba za a ce an yi murna ba domin kuwa za ka yi murna ta minti biyar na farko daga nan sai ka yi tunanin cewa bai kamata a ce wannan lamari ya faru ba tun da farko.

"Babu wani abu na murna a cikin wannan lamari saboda an sami cewa sau daya ne kacal a tsawon tarihi da aka dauki irin wannan mataki kuma wadannan kashe-kashe suna faruwa kowacce rana sannan za su ci gaba da faruwa."

Shi ma Toni yana ganin wannan labari a matsayin mai wahala.

"Kana so na samu kwarin gwiwa, lokacin da ka ji cewa an same shi da laifi kan dukkan zarge-zargen da aka yi masa za ka yi tunanin cewa lamura za su sauya," a cewarsa.

"Ina ganin irin wadannan abubuwa za su ci gaba da faruwa, kamar abin da ya faru da Ma'Khia Bryant har sai an shawo kan manyan matsaloli."

Wani dan sanda farar fata ne ya harbe Ma'Khia Bryant mai shekara 16 a jihar Ohio.

Nicholas Reardon ya harbe matashin kimanin minti 30 kafin a yanke hukunci game da kisan da Chauvin ya yi wa Floyd.

'Yana nan tare da kai'

Bidiyon kisan George Floyd ya sauya rayuwar mai sana'ar zane-zane da ke zaune a kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Laëtitia, wadda tun da farko ta yi amannar cewa rarraba bidiyon zai iya zama hanya kadai ta magance matsalar wariyar launin fata. Amma yanzu tana ganin akwai wasu karin hanyoyi.

"Duk lokacin da aka samu lamari irin wannan ina tunwa da da bidiyon abin da ya faru da Floyd," in ji ta.

"Na soma tunanin halin da wannan mutumin ya shiga yana dab da barin duniya, shin ya nemi taimakon mahaifiyarsa, kana iya ganin mawuyacin halin da ya shiga a idanunsa, kana iya ganin yadda yake ciki a karshen rayuwarsa, Ba za ka manta da irin wannan tunani ba."

Kamar yadda bidiyon ya karade duniya, haka ma batun wariyar launin fata ya ja hankalin duniya a shekara daya da ta wuce.

Toni ya ce annobar korona ta sauya muhawarar da ake yi game da wariyar launin fata fiye da yadda lamarin yake kafin barkewarta inda aka soma fafutikar neman 'yanci ga bakeken fata mai taken Black Lives Matter.

'Ba ni da 'yancin yin rayuwa'

Sai da aka yanke hukunci sannan Nia ta yarda cewa za a samu Chauvin da laifi.

Dalibar mai shekara 20 ta girma a Amurka a yayin da ake fitar da jerin sunayen mutanen da aka kashe kuma ake fafutikar nema musu hakki, amma dukkan wannan fafutika ba ta sa wa ana yanke wa masu laifi hukuncin da ya dace.

Galibin mutanen da lamarin ya shafa sunaye ne da Amurkawa da ma kasashen duniya suka saba da jin suidan aka yi batun gallazawar da 'yan sanda suke yi da kuma wariyar launin fata; Breonna Taylor, Eric Garner, Sandra Bland, Michael Brown da makamantansu.

"Na tuna kallon shari'ar Trayvon Martin sannan na tafi makaranta kuma ina koyon bangarorin gwamnati uku da yadda suke gudanar da ayyukansu," a cewar Nia.

"A lokacin da nake da 11, ina tunanin cewa, tabbas za a same shi da laifi a makon da ya gabata aka koya mana cewa idan ka karya doka za a yi maka hukunci."

Trayvon Martin bakar fata ne dan shekara 17 da ba ya dauke da makami, kuma wani mai gadi ne a makwabtansu da ke Florida ya kashe shi, amma an wanke shi daga zargin kisan kai a 2012 bisa cewa yana kare kansa ne.

Jerin wadanda ake kashewa na ci gaba da karuwa.

"Shekaru kadan bayan haka aka kashe Trayvon, Michael Brown, da kuma Tamir Rice wanda garumu daya tare da shi."

Nia ta ce iirin wadannan kashe-kashe na nuna mata cewa "ba ni da 'yancin rayuwa kwata-kwata".

George Floyd bai sadaukar da rayuwarsa ba

Wasu suna cewa 'yan siyasa sun yi amfani da sunan George Floyd domin nuna cewa ya sadaukar da rayuwarsa.

"Hakikanin gaskiya shi mutum ne da aka kashe," in ji Nia. "Sun yi tunanin cewa kisansa zai sa a rage wulakancin da ake yi wa bakaken fata."

"Matsalar ita ce yadda gwamnati take kitsa wannan batu, ba wai muna so a kama 'yan sanda da laifi bayan kashe mu ba ne - muna so ne kawai su daina kashe mu kwata-kwata."

Kusan mutum 1,000 'yan sanda suke kashewa a shekara a Amurka, a cewar wani bincike mai zaman kansa da ke bibiyar cin zalin da 'yan sanda suke yi wa jama'a. Galibinsu ana kashe su ne ta hanyar harbi.

'Yanci na daban'

Lokacin da ake kan ganiyar fafutikar Black Lives Matter a 2020, Laëtitia tana zaune a Paris a yayin da ake rusa mutum-mutumi da kuma dubbana mutane wadanda suke zanga-zanga a kan tituna domin kyamar wariyar launin fata.

Yanzu matashiyar mai shekara 29 tana zaune a birnin Kinshasa da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, inda ta koma a watan Satumba.

"Ina zaune a wurin da zan iya jin dadin zama," a cewarta.

"Akwai wan irin 'yanci a nan da ban taba samun irinsa ba, Ina magana ne a kan 'yanci na lafiyar kwakwalwa da sarari. Yaran da ke nan ba bakake ba ne, su kawai yara ne," in ji ta.

"Kawai ji nake kamar annobar korona ta dawo da ni gida saboda ba zan iya zama a Paris ba.

"Ba wai ina cewa kowa ya komo Afirka ba ne saboda ba abu ne mai sauki ba, amma idan mutum ya zauna a kasar da yake da 'yanci kuma ake sonsa ba zai koma wani wuri ba.