You are here: HomeAfricaBBC2022 12 13Article 1679699

BBC Hausa of Tuesday, 13 December 2022

Source: BBC

'Shakar gurbatacciyar iska ta sanya wa yaran Iraqi cutar kansar jini'

Hoton alama Hoton alama

Yayin da shugabannin kasashen duniya suka yi taro kan sauyin yanayi na COP 27, da kiraye-kirayen shawo kan matsalar, akwai mutane irin Ali Hussein Julood, matashi mai fama da sankarar jini, a inda yake rayuwa a wurin hakar mai da kamfanin BP ke jagoranta.

A lokacin da BBC ta gano BP bai ayyana wurin hakar iskar gas din da gurbatacce ba, Ali ne ya taimaka min fito da hakikanin abin da ke faruwa da gubatacciyar iskar da mazauna yankin ke shaka.

A shekarar 2019 ne na fara ganin wani bidiyo da aka yada a shafin Tuwita na yadda wani bakin hayaki da ya turnuke sararin samaniya, tare da ratsawa gidajen mazauna yankin. Wannan hayakin ya samo asali daga hakar mai da ake yi a yankin.

Hotunan tauraron dan adam sun nuna wurin Rumaila ne a birnin Basra, da ke kudancin Iraqi wuri mafi muni da take doka wajen hakar mai.

Tsiyayar iskar gas ba wai tana gurbata iska kadai ko muhalli ba, hatta masu shakar iskar na cike da hadarin kamuwa da cutar kansar jini, musamman ga kananan yara.

Gwamman mutanen da muka zanta da su, da ke zaune a yankuna biyar kusa da inda ake hakar man kamar Rumaila, sun ba mu labari iri guda, suna da 'yan uwa ko aminan da suka yi fama da cutar kansa, musamman kansar jini.

Daya daga cikinsu shi ne Ali, mai shekara 18, mahaifinsa ya sayar da duk abin da ya mallaka domin samun kudin kai dan shi kasar Turkiyya, wanda ke fama da cutar kansa.

Ali ya shaida mana asibitin kansa da ke da shi a Basra ya cika, yawancin mutanen da ke zaune a yankin da ake hakar mai ne.

Rumaila mazauni ne na dubban mutane, an kuma yi masa lakabi da ''Gari mai inuwa'', saboda babu komai na ci gaba ko more rayuwa a ciki. Amma ga Ali da abokansa, sun radawa garin suna ''makabarta.''

''Mun yi wasan kwallon kafa, amma a lokuta dole mu gudu gida saboda hayakin da ke turnuke sararin samaniya tada karamin hadari, dakyar muke shakar iska, sannan shi ma man ya kan malala wurinmu, ko ma ta sama tamkar ruwan sama,'' in ji Ali.

"A lokacin da na shaida wa likita a asibitin Yara masu cutar kansa da ke Basra cewa ina zaune a kusa da wurin hakar mai, budar bakinsa cewa ya yi; ''Wannan ne babban dalilin ciwonka.''

Amma ba a taba wallafa wani bincike da aka yi na kansa a yankin ba. Daga bisani mun gano gwamnatin Iraqi na danne duk wasu bayanai game da halin tabarbarewar fannin lafiya da lafiyar kanta ga mazauna Basra. Amma wani kundi da aka kwarmata mana, mun gano yawan masu kansa a Basra ya ninka adadin da gwamnati ke fada har sau uku.

Mutanen da ke aiki da zama Rumaila, sun turo mana bidiyon yadda rayuwa ta ke ga mazauna wannan wurin, amma an ki amince mana zuwa domin daukar hoto ko bidiyo da kanmu.

Bukatar da muka shigar ta neman izinin aiki a yankunan daga hukuma ba ta yi nasara ba, mun yi hakar har sau biyar, wurin mai girman sukwaya mita 1,800 ya kai wata 'yar karamar kasa, an kuma girke masu gadi babu iyaka.

Akwai kuma wurin binken ababen hawa, bayan nan akwai 'yan sandan da ke karewa wurin na wani kamfani mai zaman kansa.

Baya ga wadannan wuraren bincike da tsaro, can ta baya kuma kungiyoyin masu dauke da makamai da suka mamaye siyasar Iraqi a kudancin kasar, da kuma ke amfana da man da ake hakowa su ma sun ja ta su dagar.

Hanya daya da ta rage mana mana na shiga Rumaila, ita ce ta bad-da-kama. Muna son daukar bidiyon abin da ke faruwa, muna son daukar bidiyon yadda iskar gas ke fita da yadda mai ke malala tare da bata filaye da muhallan mazauna yankin.

Aikinmu na yi tare da kwararre kan fannin, kuma sai da muka yi gwajin yadda aikin zai kasance a saman ginin ofishin BBC da ke Landan. Kwararren ya ba mu shawarar mu yi amfani da wasu bututan shakar iska, ta za a jona kananan tukunyar iskar shaka da matacin da yake tace gurbatacciyar iskar.

Mun kuma yi aiki tare da masani kan muhalli daya tilo da ake da shi a yankin, Farfesa Shukri Al-Hassan, domin yin gwaji ga mazauna yankin da makofta daga filayen hakar mai hudu da ake da su.

Mun kuma dauki samfurin fitsarin yara, domin gwaji da zai gano ko sun shaki iskar maras.

Sakamakon gwajin da aka yi kan yara 52, ya nuna yadda sinadarin naphthalene ya yi yawa a cikin fitsarinsu. Kwararren da ke taya mu bincike ya gano akwai ribi uku na wani sinadari da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin aki.

<>Me ake nufi da tsiyayar iskar gas?

•Abin da ake nufi da kona Gas, shi ne kona mai kai-tsaye lokacin da aka hako tun ya na danye, musamman ga masu hakar mai.


•Kamfanonin mai sukan yi hka saboda dalilai na tsaro, watakila domin rage karfin gas da ke cikin tukwanen karkashin kasa, da kariya daga tashin gobara, sukan kuma kona gs domin alkinta kudi, su na kuma amfani da shi haka nan domin sayar wa wasu kasashe.


•Kona Gas na taimakawa wajen gurbata muhallii, da sauyin yanayi, da sakin kusan dan miliyan 400 na sinadarin carbon dioxide iska, kamar yadda ta faru a shekarar 2021, adadi mafi yawa da ya zarta wanda Birtaniya ke fitarwa a shekara.


•Kona gas na janyo yaduwar sinadaran benzene, naphthalene da bakin carbon, wanda ka iya shafar lafiyar wadanda ke zaune kusa da wurin.

Bayan BBC ta sako fim din da ta yi, ministan mai na Iraqi, Ihsan Abdul Jabbar Ismail, ya sha alwashin duk wani yanki da aka kona gas a Rumaila, za a tabbatar an gyara shi zuwa shekarar 2026.

Amma babu wani ci gaba da aka samu, amma lokacin da zai bar aiki, a taron manem labarai ya ce dukkan takardun da aka fara shiri kan batun sun yi batan dabo.

Babu tabbacin wanda ya ke da alhakin kula da magance kona iskar gas. Gwamnatin Iraqi ce mai filayen da ake hakar mai da kona shi, amm kuma kamfanin BP ne ya ke tafiyar da hi da wasu kamfanoni msu zaman kan su.

Ministan mai na wancan lokacin Mr Abdul Jabbar Ismail, ya shaida wa BBC cewa hakkin gyaran wurin ya rataya a wuyan BP, da tabbatar abin da ya dace tare da Rumaila Operating Organisation [Roo] -wanda BP ne ya samar da shi da ya zuba jarin kashi 48 cikin 100.

Masu kwarmata bayanai cikin ma'aikatan BP sun tunkare mu da batutuwa da dama ciki har da ikirarin mummunan halin da suke ciki a wurin aiki.

Wani tsohon ma'aikacin BP a Rumaila, da muka sakya sunan shi, ya shaida wa BBC cewa; "BP ne jagaba a aikin hakar mai, hakkinsa ne ya shaida wa gwamnatin Iraqi a sanya matakai masu inganci na kariya da yanayin aiki da kula da wurin hakar ma'adinan na Rumaila.''

Ya ci gaba da cewa halin da aka gani a Rumaila somin tabi ne, idan aka kwatanta da yanayin da suka yi aiki, babu wata cikakkiyar kulawa.

Mun yi kokarin jin ta bakin BP kan wannan ikirari amma bai ce uffan ba kan hakan.

Tsohon ma'aikacin ya ce gazawar gyaran wurin da ingantattun na'urorin zamani ya janyo ana yawan samun malalar mai da tsiyayewar iskar ga. Wannan korafi shi yawancin ma'aikatan BP tsofaffi da sababbi suka yi.


Shaidun sun nun wa BBC bidiyon yadda aka samu malalar mai da iskar gas a lokuta daban-daban.

Mai magana da yawun BP ya ce ''Ina son shaida muku cewa wannan zargi ne maras tushe bare makama, saboda batun kariyar lafiyar ma'aikata shi ne abu na farko da kamfanin BP ke kokarin cimma a Ramalla. Tun lokacin da BP ya fara aiki a Iraqi, da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, mun yi kokari da kyau na tabbatar da hakan, ba ma wasa da lamarin ma'aikata da jama'ar yankin."


Ga yara kamar Ali, da ke fama da kansar jini saboda shakar gurbataccen hayaki, garkuwar jikinsa ta yi rauni, ya daina zuwa makaranta, ba ya iya wasanni tare da abokinsa, duk da cewa ya taba wakiltar makarantarsu a wata gasar kwallon kafa da aka shirya, rayuwarsu ta tawaya.

Yawancin yaran da suke fama da cutar kansa da BBC ta gani, sun dade da mutuwa, ciki har da Fatima, mai shekara 13 da Mustafa, wanda gidansu ke kusa da wurare biyar n hakar mai a Rumaila, akwai Benin mai shekara biyar da ke kusa da Rumaila, wadda yayanta ya jima da rasuwa.

Ali ya sha zuwa gaba-gadi kamfanin BP domin a ba shi diyya, don biyan kudin makaranta. Sai dai ya ce ma'aikacin kamfanin Roo ya taba ziyartars, kwana guda bayan haska shirin binciken BBC kan lamarin, Ali ya sake tambyarsa batun biyan shi diyya.

''Na shaida masa halin da na ke ciki na rashin lafiya da batun dain zuwa makaranta, saboda gurbatar muhalli da hayakin na shaka da illar hakan ga lafiya ta. Tun daga wannan rana ban kara jin duriyarsa ba''.

BP ya ce bi dace ya yi tokaci kan wani kamfani mai zaman kanshi ba, musamman tsakanin ma'aikatan Rumaila da mazauna yankin, kamar yadda suka shaidawa BBC. Daga bisani BP ya ce ya na aikin hadin gwiwa domin tabbatar da sun duba lamarin da idon basira.

Gabannin fra binciken, BP ya shaida mana kamar yadda doka ta tanada sun kai rahoton malalar mai da tsiyayar iskar gas da kona shi ga inda ya dace (Rumaila kenan), kuma su na duba batun da idon rahama.

Sai dai wasu da suka ba mu bayanai cikin sirri, sun yi kiyasin idan ana son rage kona mai a Rumaila, ana bukatar kashe kudi da ya kai dala miliyan 3 zuwa 5 idan har ana son magance matsalar. Sai dai a makon da ya gabata, BP ya sanar da samun ribar dala biliyan 8 a rubu'in karshe na wannan shekarar.

Karin rahoto daga Jess Kelly da Esme Stallard