You are here: HomeAfricaBBC2021 03 30Article 1219411

BBC Hausa of Tuesday, 30 March 2021

Source: bbc.com

Sergio Aguero zai bar Manchester City a karshen kaka

Dan wasan Manchester City wanda ya fi kowa cin kwallo a tarihinb kungiyar Sergio Aguero zai bar kulub din a kakar wasanni ta bana, kamar yadda kungiyar ta sanar.

Kwantaragin dan wasan Argentinan mai shekara 32 za ta kare ne a wannan kakar kuma ya bayyana cewa ba zai sabunta ta ba.

Aguero ya koma kungiyar City ne a 2011 daga Atletico Madris, kuma ya ci kwallo 257 a wasanni 384 da ya buga a kungiyar.

Za a girmama shi ta hanyar gina mutum-mutuminsa a bakin kofar shiga filin wasa na Etihad, tare da na Vicent Kompany da kuma David Silva.

"Duk abin da aka fada kan gudun muwar Aguero a City cikin shekaru 10 da ya yi ba a yi karya ba," in ji shugaban kungiyar Khaldoon Al-Mubarak.

"Gwarzantakar shi za ta kasance abar tunawa a wurin duk wani mai son wannan kungiya ta Manchester City wata kila da sauran mutanen da suke kaunar kwallon kafa."