You are here: HomeAfricaBBC2021 05 31Article 1274821

BBC Hausa of Monday, 31 May 2021

Source: www.bbc.com

Sergio Aguero ya koma Barcelona daga Manchester City

Sergio Aguero, dan wasan gaba na Argentina zai koma Barcelona Sergio Aguero, dan wasan gaba na Argentina zai koma Barcelona

Dan wasan Argentina Sergio Aguero ya koma Barcelona da taka leda.

Ɗan wasan ya ƙulla yarjejeniyar shekara biyu da Barcelona kuma zai koma ƙungiyar ne idan ƙwangilarsa ta ƙare a Manchester City a ƙarshen watan Yuni.

Barcelona ta tabbatar da ɗauko ɗan wasan a shafinta na Twitter inda ta rubuta sunansa tare da wallafa hotonsa sanye da rigar ƙungiyar.