You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829084

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Sergi Roberto ya buga wa Barcelona wasa na 350.

Sergi Roberto Sergi Roberto

Ranar Lahadi Barcelona ta doke Cadiz 2-0 a wasan mako na biyu a gasar La Liga, kuma karawa ta 350 da Sergi Roberto ya yi a dukkan fafatawa.

Roberto, ya fara yiwa Barcelona wasa cikin Nuwambar 2010 a karawar da kungiyar Camp Nou ta ci 5-1 a Copa del Rey.

Amma a kakar 2010/11, ya fara yiwa Barca wasanni a dukkan karawa har da fuskantar Real Madrid a Champions League, inda Barca ta ci fafatawar.

Tun daga lokacin ya zama kashin bayan kungiyar, wanda ke buga wasannin tsakiya da kuma daga gefen fili.

Tun da ya fara buga wa Barca tamaula a 2010, kawo yanzu ya ci kwallo 16 ya kuma bayar da 40 aka zura a raga.

Wanda ya yi kaka 12 a Camp Nou, Roberto ya lashe kofi 25 a kungiyar har da bakwai a La Liga da biyu a Copa del Rey da kuma Champions League biyu.

Sauran kofunan da Roberto ya lashe a Barcelona har da Spanish Super Cup shida da European Super Cup biyu da kuma World Club Cup biyu.

A kakar nan Barcelona ta bai wa Roberto mukamin kyftin, saboda haka yana da damar daga kofuna a karshen kakar nan.