You are here: HomeAfricaBBC2021 05 02Article 1248607

BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Sarauniyar Zulu Mantfombi Dlamini ta mutu wata guda bayan soma mulki

Sarauniya Shiyiwe Mantfombi Dlamini Zulu Sarauniya Shiyiwe Mantfombi Dlamini Zulu

Iyalan masarautar kabilar Zulu a Afirka ta Kudu sun sanar da mutuwar sarauniyarsu Shiyiwe Mantfombi Dlamini Zulu wata guda kacal bayan zama shugabar rikon kwarya ta masarautar.

A watan jiya ne Sarauniya Mantfombi, mai shekaru 65, ta zama shugabar rikon kwarya ta masarautar kabila mafi girma a kasar, bayan mutuwar mijinta Sarki Goodwill Zwelithini.

Firaiministan sarauniyar ya ce mutuwarta ta zo wa iyalan da mamaki kuma "mun yi babban rashi."

Da ma dai ba a a riga an nada wanda zai gaji kujerar sarkin ba.

"Cikin halin kaduwa da bakin ciki, iyalan Masarauta na sanar da mutuwar ba-zata ta Mai Martaba Sarauniya Shiyiwe Mantfombi Dlamini Zulu, mai rikon masarautar kasar Zulu," in ji sanarwar da firaiminista Yarima Mangosuthu Buthelezi ya fitar.

Ya ce yana son ya tabbatar wa da mutane cewa "ba za a samu gibilin shugabanci ba a kasar Zulu."

A makon da ya gabata ne aka kwantar da Sarauniya Mantfombi a asibiti sakamakon wata rashin lafiya da a bayyana ba, kamar yadda kafar yada labarai ta Afirka ta Kudu ta bayar da rahoto.

An nada ta a wannan matsayi a ranar 24 ga watan Maris, bayan mutuwar mijinta Sarki Zwethilini mai shekaru 72 - a wani asibiti bayan ya sha fama da ciwon suga.

Wace ce Sarauniya Mantfombi?

Sarauniya MaDlamini Zulu ta rike matsayi mafi girma a cikin matan sarkin, saboda ta fito ne daga gidan sarauta.

Kuma kanwar Sarkin Eswatini Mswati na uku ce, sarki mai cikakken iko kadai a Afirka

Sarauniya MaDlamini Zulu na da 'yaya takwas - da suka hada da maza biyar - da suka haifa da marigayi sarkin.

Rahotanni na cewa za a nada babban dansu, Yarima Misuzulu, mai shekara 47, domin maye gurbinta.