You are here: HomeAfricaBBC2023 12 07Article 1894565

BBC Hausa of Thursday, 7 December 2023

Source: BBC

Santos ta faɗa ƙaramar gasar Brazil karon farko cikin shekara 111

Gwarzon duniya Pele a lokacin da yake zira kwallo ma Santos Gwarzon duniya Pele a lokacin da yake zira kwallo ma Santos

Kungiyar Santos ta Brazil da Pele ya buga wa ƙwallo ta faɗa ƙaramar gasar ƙasar karon farko cikin shekara 111.

Rashin nasarar da ƙungiyar ta yi da ci 2-1 a gida a hannun Fortaleza a wasan ƙarshe na wannan kakar na nufin ƙungiyar ta faɗi daga Serei A, babbar Gasar Brazil kenan.

A lokacin gwarzon duniya Pele, Santos ta lashe kofuna 12 na gida da lig shida da kuma Copa Libertadores, tsakanin shekarun 1950 zuwa da 60.

Dan wasan da ya lashe kofin duniya sau uku ya mutu ne a bara yana shekara 82.

Santos wadda anan ne Neymar da ya fi ciwa Brazil kwallo a tarihi ya yi wasa, ta rika fuskantar matsalar kudi a 'yan shekarun nan.

Palmeiras ita ce ta lashe gasar karo na biyu a jere, sau 12 kenan jimilla - biyo bayan kunnen dokin da Cruzeiro ta yi.

Flamengo da Sao Paulo su ne ƙungiyoyi biyu kacal da ba su taɓa faɗawa ƙaramar gasar Brazil ba a tarihi.