You are here: HomeAfricaBBC2023 07 01Article 1795940

BBC Hausa of Saturday, 1 July 2023

Source: BBC

Sama da janar-janar 100 za su yi ritaya a sojin Najeriya

Hoton alama Hoton alama

Kimanin manyan hafsoshin soja 100 da suka hada da janar-janar, na sojin kasa da na sama da kuma na ruwa na Najeriya za su yi ritayar dole sakamakon nadin sabbin hafsoshin tsaro da shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya yi a baya-bayan nan.

Baya ga shirin ritayar da ake shirin yi, za a kara wa jami’ai da dama girma zuwa matsayi na gaba don cike guraben da manyan hafsoshin da za su yi ritayar.

Hakan dai na faruwa ne watanni shida bayan da wasu manyan hafsoshin soja 24 da birgediya-janar 38 suka yi ritaya a watan Disambar da ya gabata bayan shafe shekaru 35 suna aiki.

Dama dai al’ada ce a aikin soja, idan aka nada na kasa a matsayin shugaba na saman su ajiye aiki, don ana fargabar watakila ba za su iya karbar oda daga wajensa ba.

Ritayar dai za ta shafi `yan aji na 36 da 37 da kuma aji na 38, wadanda suka fara aiki tun kafin wadanda aka nada, da kuma wadanda suke mataki daya da su.

Me masana ke cewa ?

Wasu masana harkar tsaro a Najeriya kamar Guruf Kyaftin Sadik Garba mai Ritaya na ganin cewa duk da al'ada ce hakan, rashinsu zai bar da gibi a bangaren tsaron Najeriya musamman a wannan lokaci da ake bukatarsu.

Sai dai ya ce yawan karin matsayi da ake yi na janar-janar din ne ke sa sau tari a duk sa'ad da aka nada shugaban da bai kai matsayinsu ba za su ajiye aiki, domin haka al'adar take.

A cewarsa ''Yanzu a wannan shekara ana maganar kusan janar-janar 130 za su tafi, don ba a sanya ido wajen karin girman, shi ya sa a yanayi irin wannan sai mutuwar kaskon ta yi yawa'' in ji shi.

Ya kara da cewa ''Idan ba a Najeriya ba ba inda ake samun tafiyar janar-janar 130 a lokaci guda''

Ya ce ko shakka babu wannan na kawo wa kasa asara, musamman idan aka duba irin tarin kudin da aka kashe musu, don haka abu ne mai ciwo a ce kasa ba ta ci moriyar shekarun da ya kamata a ce su kwashe suna aiki ba.