You are here: HomeAfricaBBC2023 07 24Article 1811156

BBC Hausa of Monday, 24 July 2023

Source: BBC

Sakamakon zaɓen Sifaniya ya ƙara cakuɗa siyasar ƙasar

Alberto Núñez Feijóo Alberto Núñez Feijóo

Jagoran jam’iyyar hamayya ta masu ra’ayin rikau ta Sifaniya Alberto Núñez Feijóo ya yi ikirarin samun nasara a zaben wuri da aka yi a kasar, amma kuma ba tare da cewa ya samu sakamakon da yake bukata ba.

Duk da cewa ya samu goyon bayan jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayin rikau, jam’iyyarsa ta Popular Party, ba ta samu rinjaye a majalisa ba.

Yanzu dai sakamakon ya nuna tsakanin masu ra’ayin rikau da kuma masu ra’ayin kawo sauyi babu wanda ya samu damar kafa gwamnati ta kansa.

Sakamkon zaben na wuri na Sifaniya ya kasance wanda kusan kowane bangare ke ikirarin nasara, amma kuma duk da cewa ya kasance kamar wanda bai kammalu ba, domin kuwa babu jam’iyyar da ta samu rinjayen da ake bukata a majalisar dokoki abin da zai bayar da damar kafa gwamnati.

Jagoran jam’iyyar masu ra’ayin rikau, People’s Party, ko PP Alberto Alberto Núñez Feijóo wanda ke cike da murna duk da yadda sakamakon ya kasance ya ce a yanzu nauyi ya rataya a wuyansa na ya kafa gwamnati saboda jam’iyyar tasa ce ta samu kujeru mafiya yawa, har ma ya bukaci sauran jam’iyyu da kada su kawo masa wani tarnaki.

Ya ce, ''babu wani shugaban gwamnatin Sifaniya da ya yi mulki bayan ya fadi zabe. Saboda haka, abokanaina, wannan dama ta hau kaina na jarraba, muna zabin da ya kasance, kuma abin da zan yi ke nan.’’

Jam’iyyar ta PP ta samu wannan nasara ne ta yawan kujeru amma ba tare da samun rinjayen da ake bukata ba a majalisar na kafa gwamnati, duk kuwa da goyon bayan da ta samu na jam’iyyra Vox ta masu tsananin ra’ayin rikau.

Jagoranta, Santiago Abascal ya ce sakamakon ba shi ne abin da ya yi fata ba;

Ya ce, ''rana ce ta damuwa , rana ce ta damuwa domin ba mu cimma burinmu na yin waje da Pedro Sanchez, daga fadar gwamnati (Moncloa Palace) kuma kila za a yi wani zaben, inda za mu iya samun yin hakan.’’

Haka shi ma dai bangaren Firaminista Pedro Sanchez, mai ra’ayin gurguzu murna yake, kamar daya bangaren duk da yadda sakamakon ya kasance, yana mai cewa hakar ‘yan hamayyar ba ta cimma ruwa ba, sun gaza.

To amma ko ba komai yadda sakamakon zaben ya kasance, ya wanke Firaministan a kan matakin da ya dauka da ya janyo ce-ce-ku-ce, na neman a yi zaben a lokacin tsananin zafi a Sifaniyar, inda yanayin ya kai maki 40 a ranar zaben a wasu sassan kasar.

Kuma duk da haka aka samu fitowa sama da kashi 70 cikin dari, saboda yadda masu zaben suka dauke shi da muhimmanci, inda wasunsu ma suka dawo daga hutun da suke domin su kada kuri’arsu cikin ‘yan gajejjerun tufafi na ninkaya.