You are here: HomeAfricaBBC2023 07 29Article 1814732

BBC Hausa of Saturday, 29 July 2023

Source: BBC

Saint-Maximin zai bar Newcastle United

Allan Saint-Maximin Allan Saint-Maximin

Dan wasan tawagar Faransa, Allan Saint-Maximin ya tabbatar da cewa zai bar Newcastle United kafin fara kakar tamaula ta bana.

Ana sa ran Saint-Maximin, mai shekara 26, zai koma taka leda a Al-Ahli mai buga gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Ya ci kwallo 13 a wasa 124 tun bayan da ya koma St James Park a Agustan 2019 daga Nice.

Newcastle ta kare a mataki na hudu a teburin Premier League a kakar da ta wuce, hakan ya sa za ta buga Champions League a bana karon farko bayan shekara 20.

Kungiyar ta koma kan ganiya karkashin koci, Eddie Howe, wanda ya karbi jan ragama wata daya da attajiran Saudi Arabia suka sayi kungiyar a Oktoban 2021.

A bara ne daraktan wasannin kungiyar, Dan Ashworth ya ce za su sayar da wasu 'yan kwallon, domin bin dokar kashe kudi daidai samu.

Kafin fara kakar bana, Newcastle ta sayi dan kwallon tawagar Italiya, Sandro Tonali daga AC Milan kan fam miliyan 55 da na Ingila, Harvey Barnes daga Leicester kan fam miliyan 38.