You are here: HomeAfricaBBC2023 09 19Article 1847300

BBC Hausa of Tuesday, 19 September 2023

Source: BBC

'Sai mun sayar da rai muke zuwa binne matattu a Sudan'

File foto File foto

Yayin da rikici a Sudan tsakanin sojoji da rundunar RSF ke ƙara ta'azzara, 'yan uwana suka binne kakata mai shekara 84, babu abin da ake gani a samaniyar maƙabartar sai giftawar harsashi a Omdurman - tsallaken Kogin Nilu daga Khartoum.

Kakata na da ciwon siga kuma jininta ya yi ƙasa, amma mun gaza kai ta asibiti a Omdurman - inda har yanzu akwai miliyoyin mutane da ke rayuwa a birnin duk da irin rikicin da yake fuskanta abin da ya sanya asibitocin a garin ba sa aiki, wasu an kori kowa da ke ciki, wasu kuma mayaƙa sun kwace iko da su.

Babu abin da suke sai karɓar mayaƙan da aka yi wa rauni a yayin faɗan da ake yi, kuma suna nan ciki birjik - harsashi da bam da ruwan gurneti ne ke yawo a saman gidajen mutane. Dalilin haka marasa lafiya ba sa iya samun damar zuwa asibiti a Omdurman.

Saboda rashin ganin likita da magani lafiyar kakata ta riƙa taɓarɓarewa.

Mun so binnenta kusa da kabarin kakana, mijinta kenan wanda ya mutu a 2005, Sai dai maƙabartar da yake tana kusa da ofishin 'yan sanda na Central Reserve.

Yanki ne da ake yaki a cikinsa babu ƙaƙƙautawa, yayin da mayaƙan RSF ke yunƙurin karɓe iko da sansanin 'yan sandan.

Sai muka ɗauki gawarta zuwa wata maƙabartar da ke yankin da babu hayaniya cikinsa, a wannan ranar sai muka yi rashin sa'a an ɓarke da yaki a tsallaken maƙabartar.

'Yan uwa da suka je binneta yaƙin ya tilasta musu ajiye gawarta a ƙasa su jira har sai da lokacin da aka samu raguwar harbe-harbe sannan suka binne ta.

Sai da suka shafe kimanin sa'o'i shida gabanin su bar cikin maƙabartar, yayin da faɗuwar rana ce kawai ke kawo sauƙin rikicin.

Da yawan 'yan uwan kakata sun maƙale a gidanta - kuma da dama sunƙi futowa daga ɗakin ne saboda faɗan da ya ɓarke a makobta, kuma rikicin ya kwashe awanni ana yi.

Amma mun yi nasarar binne ta a maƙabarta, wasu kuma sun gwammace binne 'yan uwansu a gidajensu.

Wani matashi Khalid Sanhouri da ke kaɗa jita ɗan uwansa ya binne shi ne a ƙofar gidansu wani tshon gini da ya kwashe shekaru a Omdurman.

Tsohon garin Omdurman inda Sanhouri ke zaune - yakin ya yi fata-fata da shi, saboda faɗan da dakarun RSF ke yi ba dare ba rana domin kwace iko da gadar da ta haɗe Khartoum da garin Bahri.

Ko da yaushe ana kai hare-hare ta sama da kuma harba gurneti a yankin.

An kashe mazauna yanki da dama, an kuma ruguza gine-gine da wuraren kasuwanci da yawa.

Kakata ta zauna a wani yanki na Omdurman, inda yaƙin bai shafa ba da yawa har sai daga bayan nan. Ta shaƙu da mazauna yankin da suke makwabtaka.

Shekaru 10 baya ne lokacin da rashin lafiyarta ta fara taɓarɓarewa, a wancan lokutan ɗaruruwan yara ne ke taruwa a gidanta a kowacce Juma'a, saboda tana ba su kyauta.

Da yawan waɗannan yara duk sun girma wasunsu ma da iyalai - sun riƙa shiga suna gaisuwa ga gawarta kafin a ɗauke ta zuwa maƙabarta.

Yau mako uku da binne ta, kuma tun daga nan da yawan yaran sun tsere daga muhallansu saboda yaƙin da ake yi a yankin akai-akai.

Sojoji ne ke yunƙurin murƙushe dakarun RSF waɗanda suke iko da wurare masu yawa a Khartoum.

Mahaifiyata ta tsallake rijiya da baya, kiris ya hana ta mutu.

Lokacin da taje kasuwa sayan kayan miya, sai aka kai harin jirgi maras matuƙi nesa da ita, wanda ya janyo fashewa mai girman gaske. Sai ta tsaya cak a inda take daga baya kuma ta kwanta a ƙasa.

A bayyane yake cewa ranar 24 ga watan Agusta - ranar da aka binne kakata cike take da mamaki. Ita ce ranar da Janar Abdel Fattah al-Burhan ya tsira daga tsarewar da dakarun RSF suka yi masa.

Ya samu ya fice daga hedikwatar sojoji da ke Khartoum bayan ɗaurin talalar da suka yi masa tun farkon fara wannan yaƙi a ranar 15 ga watan Afrilu.

Tun daga lokacin, Janar Burhan ya koma garin Port Sudan da zama, yake kuma tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare domin neman samun goyon bayansu a yaƙin da suke da dakarun RSF.

Ana ci gaba da tattaunawa a Saudiyya, Sai dai har yanzu Janar Burhan bai halarci zaman ba.

Yana da zance shi ma - kamar takwaransa kwamandan dakarun RSF Janar Mohamed Dagalo wanda ake kira Hemeti - dukkansu suna yi wa juna kallon maciya amnar ƙasa, sun gwammace su ci gab da faɗa maimakon tattaunawar sulhu.

Su biyun suka yi juyin mulki tare a watan Oktoban 2021, daga nan kuma suka shiga rikicin neman iko, abin da ya kai mutanensu da ɗaukar makamai su yaƙi juna.

Akwai wani abun shakku kan cewa sojoji sun ƙara yawan hare-harensu kan dakarun RSf tun bayan kawo ƙarshen tsare Janar Burhan da aka yi, wannan ya janyo ƙara samun asarar rayuwakan fararen hula.

"Kana buɗe kofar gidanka za ka ga mutane ɗauke da gawa a kafaɗunsu. abun tsoro ne wannan," kamar yadda wata mata da ta tsere daga Omdurman ta bayyana.

A dare ranar 29 ga watan Agusta, an kashe wasu mutum 10 da ke kallon kwallo a tsakiyar Omdurman bayan harba musu gurneti da dakarun gwamnati suka yi.

Da alamar ba su samu abin da suka hara ba - wataƙila wani gidan abinci da dakarun RSF suke cin abincin dare suka so hara. Amma a wannan yammaci babu wanda ya je gidan abincin.