You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816556

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

Sadio Mane ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia

Sadio Mane Sadio Mane

Bayern Munich ta sanar cewar tsohon dan kwallon Liverpool, Sadio Mane ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia.

Dan wasan tawagar Senegal, ya ci kwallo 12 a karawa 38 da ya yi wa kungiyar Jamus, wadda ta lashe Bundesliga a kakar da ta wuce.

Babban jami'in Bayern, Jan-Christian Dreesen ya ce dan kwallon mai shekara 31 ya ci karo da kalubale tun bayan da ya koma Jamus daga Anfield.

Mane zai koma taka leda tare da Cristiano Ronaldo a Al-Nassr kan fam miliyan 35 kamar yadda ake hasashe.

Irin kudin da Bayern Munich ta dauki Mane a bara kenan daga kungiyar da ke Anfield.