You are here: HomeAfricaBBC2023 09 13Article 1843070

BBC Hausa of Wednesday, 13 September 2023

Source: BBC

Sabuwar gardama ta kaure tsakanin PDP da APC kan hukuncin kotun zaɓe

Tutar APC da PDP Tutar APC da PDP

Wata sabuwar gardama ta kaure tsakanin jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma babbar jam`iyyar hamayya ta PDP bayan bayyanar wani kundi da ke kunshe da cikakken bayani a kan hukuncin da kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa ta yanke wanda ke dauke da hatimin jam`iyyar APC.

Jam'iyyar PDP na zargin cewa APC ce ta tanƙwara hukuncin, kuma wannan ne ya sa aka tsara yadda hukuncin zai kasance har ma ya fito da hatiminta.

Sai dai APC ta musanta, tana cewa ita ce ta buga hatiminta a jikin hukuncin bayan kotun ta bai wa kowa ce jam'iyya ainahin kwafin hukuncin ba tare da hatimin ba, don haka PDP zargi take yi irin na ganganci.

A dangane da lamarin ne PDP ta ce ta tsaya tsam ta yi nazarin kundin da ya ƙunshi cikakken bayanin hukuncin kotun.

Kuma a ƙarshe ta ƙare da dąsa ayoyin tambaya a kan abubuwan da ta gani tattare da kundin, wanda ya sa take zargin cewa jam`iyyar APC ce ta yi uwa da makarbiya wajen tsara hukuncin yadda take so.

Matamakin kakakin jam'iyyar ta PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi ya ce, hatimin APC da ke jikin kundin hukuncin ya tabbatar da zargin da PDP ke yi cewa da ma can hukuncin da kotun ta yanke na je-ka-na-yi-ka ne kawai.

"Muna zargin cewa alƙalansu sun riga sun san makomar zaɓen domin tambarin,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa, "fitar wannan ya nuna cewa suna da masaniya a kan abin da alƙalan suka fitar.

''Wannan kuma za a same shi ne daga kwamfutar wanda yake da masaniya.

''Shi muke ƙalubalantar cewa ta ina ne suka samu wannan hujja me ya tabbatar musu dacewa su ne suka yi nasara ko suka yi galaba akfin ainahin shari'ar a fito da ita?" A cewar matimakin kakakin na PDP.

Sai dai jam'iyyar APC a nata martanin, ta ce PDP rikici kawai take yi irin na ganganci.

A cewar, Daraktan yaɗa labaran APCn Mallam Bala Ibrahim a tattaunawarsa da BBC.

Ya ce, "shakiyanci ne da gangan domin kawai a gwara kawunan mutane a ruɗa su su kasa fahimtar gaskiyar magana."

"Amma ita jam'iyyar PDP ta sani cewa ba haka abin yake ba. Ita kotu wacce ta yanke hukuncin duk lauyoyin da suka gabatar da ƙara a gabanta ta aike musu da hukuncin da ta yanke, tabbataccen hoton takardar da aka rubuta abin a kai."

Ya ƙara da cewa, "To APC da ta samu wannan sakamako Presidential Campaign Councin na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka tashi buga wannan takarda da ta zo daga kotu sai suka buga a kan takardar da ke da hatimin jam'iyya.''

''Amma ita PDP idan za ta faɗi gaskiya ai sai ta faɗa cewa ga yadda aka turo mata daga kotu babu wannan hatimi na jam'iyya," in ji shi.

A ƙarshen makon da ya wuce ne kotun sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasar ta yanke hukunci a kan ƙarar da jam`iyyar PDP da Labour da kuma APM da 'yan takaransu suka kai gabanta.

Ƴan hamayyar sun ƙalubalanci nasarar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen da aka yi a watan Fabarairun da ya wuce.

Amma a hukuncin da alƙalan kotun suka yi, ƙarƙashin jagorancin mai shara'a Haruna Tsammani, sun tabbatar da nasarar Bola Tinubu…

Sannan ƙarshen makon kotu ta danƙa wa jam`iyyu da `yan takarar kundin bayanin hukuncin.

Jam'iyyar PDP da Labour sun yi watsi da hukuncin inda suka lashi takobin danganawa da Kotun Ƙoli.

Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta ce ya kamata su daddara, su hada-kai a raya ƙasa.