You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1761023

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Ronaldo ne na daya a samun kudin shiga tsakanin masu wasanni

Cristiano Ronaldo Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya zama na daya a samun kudin shiga a duniya tsakanin masu sana'ar wasanni.

Karon farko da ya taka wannan matakin tun bayan 2017, sakamakon da ya koma Al Nassr ta Saudi Arabia da taka leda a Janairun 2023.

Mujallar Forbes ta wallafa cewar dan kwallon tawagar Portugal, mai shekara 38 ya samu $136m (£108.7m) a wata 12 da ya wuce.

Kwantiragin da ke tsakaninsa da Al Nassr ta kai sama da yuro 200m kwatankwacin (£176.5m) a kowacce shekara.

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi shine na biyu da Forbes ta wallafa mai kudin shiga $130m (£103.9m).

Cikin jerin goman farko da Forbes ta wallafa har da dan kwallon kwandon Amurka, LeBron James da dan damben boksin, Canelo Alvarez.

Roger Federer shine kadai wanda ya yi ritaya, amma yana cikin jerin 10, wanda yake na tara, fitatcen dan kwallon tennis a duniya.

Forbes ta hada kididdigar da ta hada da albashi da ladan wasa da tallace-tallace da sauran kudin da dan wasa ke samu.

Jerin 'yan wasa 10 da suke kan gaba a samun kudin shiga a duniya a 2023:

1. Cristiano Ronaldo, football: $136m (£108.7m)

2. Lionel Messi, football: $130m (£103.9m)

3. Kylian Mbappe, football: $120m (£95.9m)

4. LeBron James, basketball: $119.5m (£95.5m)

5. Canelo Alvarez, boxing: $110m (£87.9m)

6. Dustin Johnson, golf: $107m (£85.5m)

7. Phil Mickelson, golf: $106m (£84.7m)

8. Stephen Curry, basketball: $100.4m (£80.2m)

9. Roger Federer, tennis: $95.1m (£76m)

10. Kevin Durant, basketball: $89.1m (£71.2m)