You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218598

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: bbc.com

Robert Lewandowski: Dan wasan gaban Poland ba zai buga fafatawarsu da Ingila ba

Dan wasan gaban Poland Robert Lewandowski ba zai buga fafatawar da za su yi da Ingila a Wembley ranar Laraba ba ta neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2022 sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa.

Dan wasan na Bayern Munich mai shekara 32 ya rika dingishi har sai da aka fitar da shi daga fili a wasan da suka yi nasara a kan Andorra da ci 3-0 ranar Lahadi inda ya zura kwallaye biyu.

Hukumar kula da kwallon kafar Poland ta ce zai yi jinyar da ta kai ta kwana goma saboda raunin da ya ji.

Yanzu sai Lewandowski ya yi kokarin samun sauki idan yana son buga wasan da Bayern za ta yi da Paris St-Germain na dab da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai nan da kwana tara masu zuwa.

Ya tafi Jamus domin a sake duba lafiyarsa da kyau.

Join our Newsletter