You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896701

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

Rikicin kama-wuri-zauna ya haddasa fargaba a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

File foto File foto

A kwanakin nan ne wata katafila ta rushe wata makaranta a Khirbet Zanuta, wani ƙaramin ƙauyen Falasɗinawa a tsaunin hebron da ke kudancin yankin.

Duka ƙauyen ya cika da tarkace da ƙura a lokacin da muka kai ziyara.

Ƙauyen ya zama kufai, yayinda kimanin mutane 200 da ke zaune a ciki suka tsere kimanin wata guda da ya wuce, bayan matsin lamba da suka sha daga Yahudawa 'yan kama wuri zaune da ke zaune kusa da ƙauyen, duk kuwa da haramcin hakan ƙarƙashin dokokin Isra'ila da na duniya.

Wasu tarkacen ƙarafa da ke cikin ɓaraguzan makarantar a ƙauyen Khirbet zanuta. Cikin manyan baƙaƙe an rubuta ''Tallafin jin ƙan Falasdinawa na cikin hatsarin ficewa daga Gaɓar Yamma da Kogin Jordan''.

Alamar na nuna waɗanda suka bayar da kudin gina makarantar. Ƙungiyar Tarayyar Turani ce ta jagoranci aikin a cikin ayyukan ƙungiyar, haka kuma an samu tambarin gidan sarautar Birtaniya tare da rubutun kalmomin 'Ƙaramin Ofishin jakadancin Birtaniya a Birnin Kudus.

Nadav Weiman ya je ƙauyen tare da BBC. Tsohon jami'an sojan Isra'ila na musamman ne, wanda a yanzu ɗan gwagwarmaya, da ke cikin ƙungiyar masu adawa da mamayar yankunan Falasɗinawa.

"Suna ta lalata ƙauyukan Falasɗinawa, da duka manoman Falasɗinawa tare da sace musu abubuwan da suka noma tare da yunƙurin buɗe korar Falasdinawa daga yankin, saboda suna son zama a wurin su kaɗai ba tare da Falsdinawa ba''.

Sojojin Isra'ila biyu sun zo domin domin gudanar da bincike kan abin da muke yi a wajen. Daya daga cikinsu ya Faɗa wa wani ɗan Isra'ila da ke cikin tawagar BBC cewa ya zama ma-ci amanar ƙasa saboda ya ziyarci Falasɗinawa

Sun ɗauke mu a bidiyo, sai dai ba su nuna jin daɗi kan abin da ya faru a Khirbet Zanuta ba.

A lokacin da na tambayi 'yan sanda ko suna bincike kan abin da ya faru da makarantar ƙauyen, sun turo mana da saƙon email da ke cewa suna jiran ƙorafi game da hakan. Lauyan mutanen ƙauyen har kara ya shigar a kotun ƙoli.

A kwanaki ukun da muka yi muna ziyara a abar Yamma da Kogin Jordan, Falasɗinawa sun faɗa mana cewa tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, Yahudawa 'ya kama-wuri-zauna sun riƙa yawaita hare-hare.

Yahudawan 'yan kama-wuri-zauna sun tsananta hare-haren ciki har da harbin Falasɗinawa a yankin Ga bar Yamma da Kogin Jordan.

Hare-hare da dama na faruwa, yayin da manyan ƙawayen Isra'ila, wato Amurka da Birtaniya, suka yi Allah wadai da hare-haren 'yan kama-wuri-zaunan masu tsattsauran ra'ayi, tare da kiran a gurfanar da wadanda aka kama da laifi a gaban sharia'.

Muntassar Mhilat ne ya ɗauki bidiyon ha kiƙiƙanin yadda 'yan kama wuri-zauna ke kai wa Falasdinawa hari.

Muntassar matashi wani matashi ne daga dangin Bedouins da ke zaune a hamadar Judean mai nisa daga Jericho.

Kusan sau 20 Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna na kai wa gidansu hari.

Muntassar ya ɗauki bidiyonsu a lokacin da suke nuna su da makamai.

"Ya harbe kawuna, daga nan sai na taho wajensu domin na fuskance su. Mun fuskanci juna inda muka riƙa musayar yawu da faɗe-faɗe. Kuma ina ɗaukarsa bidiyo, daga nan ne wasu karin Yahudawa 20 suka zo.'

Bidiyon ya nuna Bayahuden na riƙe da bindigar ƙirar M-16 yana nuna ta ga iyalan gidan su Muntassar. Daya daga cikin matan da ke wajen, mai suna Umm Omar, riƙe da ɗanta ɗan wata guda sun kusa mutuwa.

"Sun kai hari gidanmu, tare da sace mana tumaki, sun yi wa 'ya'yana barazana da bindiga sannan nima suka yi min. Dana suka buge ni tare da kamwar mijina. Na ɗauka ma yanka mu za su yi,'' in ji Umm Omar.

Ba wanda aka kashe. Iyalan sun ce Yahudawan sun yi musu ƙagen sace mutu awaki. Mutumin da ya nuna mu da bindiga na sanye da rigar 'yan sanda.

Wani abu da ake ƙorafi a kai shi ne mayar da 'yan kama-wuri-zaunan cikin aikin soji bayan harin 7 ga watan okotoba ta Hamas ta kai, kuma suna saɓa doka da ƙa'idar aikin kaki da makamai da ƙasar ta ba su.

Mutanen gidan su Muntassar sun gane wasu daga cikin maharan, yayin da suke zuwa daga wani ɗan ƙaramin sansanin soji da ke kusa da gidan suna farmakar mutanen yankin. Suna sane cewa nan gaba su za a kawo wa hari, kan haka ne suke cikin damuwa da fargaba.

Musgunawar da ake yi wa Falasdinawa ta shafi tattalin arziki da ƙwaƙwalensu

A kudancin Hebron, Falasdinawa manoma na yin noma da jakuna saboda Yahudawan yankin sun yi musu barazanar sace ko lalata motocin nomansu matuƙar suka yi amfani da su.

A wani ɓangaren Gabar Yamma da Kogin Jordan ɗin, a wani ƙauye da ke wajen Nablus da ake kira Burin, Ahmed Tirawi, wani manomi ne muka taras yana hango gonarsa ta bishiyoyin zaitun, waɗanda suka fara ruɓewa, sakamakon hana shi zuwa gonar da aka yi domin ya kaɗo su.

"Idan na je can gefen tsaunukan domin kaɗo 'ya'yan zaitun dina, zan jefa rayuwat cikin hatsari. 'Yan kama wuri-zaunan suna kai hari kan manoma a wurin, da hartsashi guda za su kashe ni''.

Kakar zaitun ta zo, to sai dai babu dama ciro 'ya'yan, kaka ba ta zo mana yadda muke so ba.

Mun yi magana da Yehuda Simon, wani fitaccen shugaban 'yan kama wuri-zaunan a wani ƙaramin sansani da ke Havat Gilad, kusa da Nablus. Shi lauya ne da ke wakiltar 'Yan kama wuri-zaunan da ake zargi da kainwa Falasdinawa hari.

Ya kuma amsa a lokacin da na tuntuɓe shi kan ƙorafin Falasdinawa manoma da ke yanki da suka ce an hana su girbin amfanin gonarsu, musamman 'ya'yan zaitun.

"Sojoji sun fahimce cewa Falasɗinawan na zuwa girbin ne domin tattara bayanai don shirya harin 7 ga watan Oktoba.''

Fiye da ƙarni guda da ya shuɗe, Larabawa da Yahudawa ke faɗa a kan mallakar filaye a wanna ɗan ƙaramin ƙauye.

Yaƙin da ake yi a Gaza bai kara rikicin da ake yi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ya yi kawai ba. Yadda yaƙin zai ƙare, zai shafi ƙananan yara masu tasowa da suka tsira daga wannan yaƙin.

Falasɗinawa da dama ne ke tunawa da tilasta musu ficewa daga gidajensu a shekarar 1948.

A lokacin 'yan Isra'ila sun ci nasarar yaƙin, bayan da suka samu 'yanci kai, fiye da Falasɗinawa 700,000 suka fice ko aka tilasta musu ficewa daga gidajensu da bakin bindiga.

Sabuwar ƙasar ta ƙwace dukiyoyinsu, kuma ba su bar su sun koma gidajen nasu ba.

Falasɗinawa na kiran lamarin na 1948, da bala'in ''Nakba''.

Rikicin 'yan kama-wuri-zauna tare da tabbatar da asarar gidajen Falasdinawa, babban abin da suke fargaba shi ne ƙarfin dakarun sojin Isra'ila, kuma yunƙurin 'yan kama wuri-zauna shi ne su fice daga gidajensu, inda suka amfani da rikice-rikicen da ke tattare da yaƙin Gaza domin tabbatar da haka.