You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806389

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici

Hoton alama Hoton alama

Shugabanni huɗu daga ƙasashen Gabashin Afirka ƙarƙashin Jagorancin Ƙasar Kenya sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici a Sudan, tare da amfani da dakarun yankuna don tsaron rayuwar fararen hula da kuma bayar da damar kayan agaji su isa ga miliyoyin al`umma da rikicin ya rutsa da su.

Samun amincewar ɓangarorin da suke fafatawa da juna zai yi wahala idan aka yi la`akari da yadda su ka fifita amfani da ƙarfin soja tun bayan ɓallewar rikicin a watan Afrilun bana.

Ita ma Ƙasar Masar ta shirya don gudanar da wani taro tsakaninta da ƙasashen da su ke maƙotaka da Sudan don lalubo hanyoyin warware rikicin tsakanin Sojojin Sudan da Dakarun RSF.

Shugaban Sojojin Ƙasar Janar Abdel Fattah al-Burhan shi ne ya ke iko da da dama daga cikin yankunan Gabashi da kuma Tsakiyar Sudan yayin da Dakarun RSF su ke iko da wasu sassan Gabashi da Tsakiyar Ƙasar tare da fafutukar riƙe ikon sansaninsu a Khartoum.

An zargi Dakarun RSF Ƙarƙashin Jagorancin Janar Mohamed Hamdan Dagolo da kisan kai da fyade da kuma karɓe ikon asibitoci.

Bama-baman da Dakarun RSF su ka dasa a babban birnin kasar sun jikkata fararen hula da dama. Kafafen yaɗa labarai sun bayyana yadda rikici ya mamaye Yammacin Sudan.

Dakarun RSF hadin gwiwa da Larabawa Ƴan Ta Da Ƙayar Baya sun kori dubban Ƴan Ƙabilar Masalit daga garuruwansu a Yammacin Dafur.

Sun ƙone Fadar Sarkin Garin tare yin garkuwa da Gwamna Khamis Abbakar jim kaɗan bayan ya ayyana su a matsayin masu aykata kisan kiyashi.

Sama da fararen hula dubu ɗari da sittin ne suka tsre daga Sudan ta iyakar Tchadi.

Dakarun na RSF sun kewaye garuruwan al-Fashir da Nyala bayan sun sace kayan jama`a Zalingei.

Da dama daga cikin mazauna Dafur na fargabar wannan ta`asa shiri ne na mayar da yankin mai ƙabilu da dama zuwa na Larabawa zalla.

Bukatar gaggawa a Yammacin Darfur ita ce kariyar farar hula. Tawagar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Afirka a Darfur sun ƙudiri wannan aniya a baya, amma an janye shirin shekaru biyu da suka gabata.

Dakarun RSF sun yiwa El-Obeid dake Arewacin Jihar Kordofan kwantan ɓauna.

Makwonni biyu bayan fara yaƙin, ƙasashen Saudiyya da Amurka sun kaddamar da shirin tattaunawar tsagaita wuta a Jeddah.

Saudiyya da Amurka sun sanar da shirin sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutar, za kuma su gayyato Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a matsayinta na wacce ake ganin ta na da alaka da Dakarun RSF kodayake babu martani daga ƙasar game da zarginta da samarwa RSF makamai.

Watan da ya gabata Shugabannin Ƙasashen Gabashin Afirka suka ƙaddamar da shiri na musamman Igad, sakamakon rashin gamsuwarsu da irin rawar da Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta ke takawa a rikicin na Sudan.

An zaɓi Shugabannin Ƙasashen Kenya da Habasha da Sudan ta Kudu da kuma Djibouti a matsayin waɗanda za su jagoranci Tsagaita Wutar da kuma nemo hanyoyin da za a bi wajen shigar da kayan agaji tare da tattaunawa a siyasance don mayar da Dimukuraɗiyya a Sudan.

Shugaba William Ruto na ƙasar Kenya wanda ke jagorancin ƙungiyar ya bayyana yaƙin a matsayin rashin sanin ciwon kai, ya kuma yi Allah Wadai da bangarorin da suke rikicin da juna ta hanyar amfani da ƙarfin soja wajen lalata ƙasar da yiwa fararen hula kisan gilla, kuma ya tsoratar game da faruwar kisan kiyashi a Dafur.

Wannan rukunin Shugabanni sun gudanar da taro a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha a ranar Litinin inda su ka dauki matakin farko na shirya rundunar shiga tsakani a yankin.

Hanya ta biyu kuma ita ce yin aiki tare da Amurka da Saudiyya don gudanar da taron gaba-da-gaba tsakanin Janar Burhan da Hemedti don tabbatar da tsagaita wuta.

Batu na uku shine tsarin siyasa mai haɗaka daga watan Agusta. Hakan na bukatar haɗa wakilan farar hula wuri guda, da kuma ba su isassun goyon bayan siyasa, ta yadda za su samu damar yin shawarwari na hakika, a wani bangare na tabbatar da ganin Sudan ta koma turbar dimokuradiyya.

Sai dai Janar Burhan ya ki amincewa da shirin, ya na mai cewa Mista Ruto ya fifita kungiyar RSF. Ya kuma zargi shugabanin wasu jam'iyyun farar hula da hada kai da Janar Hemedti yayin da aka zargi Janar Burhan da tattara Kungiyoyin Islama a bangarensa.

Sojoji na ikirarin samar da halastacciyar gwamnati, duk da cewa sun karɓi mulki a wani juyin mulki da RSF a shekarar 2019, kafin shugabanninsu su gaza al`amarin da ya haifar da yaƙin basasa.

Mista Sisi ya na kallon Janar Burhan a matsayin na hannun damansa a Sudan, kuma a shirye ya ke da komowar kungiyoyin Islama a Sudan waɗanda ke samun goyon bayan Qatar da Turkiyya.

Sai dai akwai fargabar masu adawa da shirin zaman lafiya na Afirka da na Larabawa za su haifar da tarnaƙi a shirin.

An jingine Majalisar Dinkin Duniya a wannan batu, an zaɓi wakilin majalisar a Sudan Volker Perthes saboda ƙwarewarsa domin ya bayar da gudummawa wajen hadin kan ɓangarorin da suke gaba da junan su amince a ƙaddamar da gwamnatin hadin kai.

Al'ummar Sudan da dama sun bayyana rashin gamsuwa game yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kasa maido da zaman lafiya a Sudan.

Wasu daga cikin al`ummar Ƙasar sun zargi Ƙungiyar Tarayyar Turai da goyon bayan dakarun RSF a baya don su samu damar yin iko da iyakokin kasar, batun da kungiyar EU ta ƙaryata.

Ƙalubalen samar da zaman lafiya a Sudan ba ƙarami ba ne. Wannan shiri na Shugabannin Afirka ya na kunshe da ƙalubale duk da cewar ya na da fa`ida. Bayan rashin samun haɗin kan ɓangarorin da suke rikici da juna su fahimci cewar amfani da ƙarfin soja ba shi ne mafita ba.