You are here: HomeAfricaBBC2023 08 22Article 1829876

BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023

Source: BBC

Rikicin Sudan : Farashin bindiga AK-47 ya faɗi warwas a kasuwar bayan fage

Hoton alama Hoton alama

Farashin bindiga samfurin AK-47, guda daga cikin makaman yaƙin da aka fi amfani da su ya faɗi warwas da kashi 50 a watannin da suka gabata a kasuwar bayan fage dake Khartoum babban birnin kasar, yanzu ana sayenta akan dala 830.

Wani dillalin makamai ya ɗora alhakin faɗuwar farashin bindigar kan yadda bindigar mai laƙanin Kalashnikov ta ƙasar Rasha ta cika kasuwannin bayan fage bayan ɓallewar rikici a Sudan a watan Afrilu.

Ana ci-gaba da gwabza faɗa tsakanin sojoji da dakarun RSF a kan titunan biranen Khartoum da Bahri da kuma Omdurman waɗanda sune manyan biranen ƙasar.

Wani mai saye da sayar da bindigogi ya bayyana cewar ya na sayen bindiga daga tsoffin sojoji waɗanda da dama daga cikinsu dakarun RSF ne a yanzu.

Buƙatar bindigar ta yi yawa bayan yaƙin Bahri wanda aka gwabza a tsakiyar watan Yuli, watannin uku da fara rikicin da ya ɗai-ɗai-ta Sudan.

Gawarwaki sun cika titunan birnin Bahri bayan sojojin gwamnati sun yi asarar rayukan jami`ansu sakamakon arangama tsakaninsu da dakarun RSF waɗanda suke riƙe da wasu bangarori na biranen Bahri da Khartoum da kuma Omdurman.

"An kama sojoji da dama yayin da aka kashe wasu, al`amarin da ya sa masu sayar mana da bindigogi suka samu wadatattun makamai," inji wani mai dillalin bindigogi.

Hakan na nufin ba zai sake dogaro da kasuwar bayan fage ba, wacce take shigo da bindigogi ta kasar libiya, abinda ya bayyana yadda rashin bin doka da oda ya dabaibaye yankin Arewacin Afirka tun bayan hamɓarar da gwamnatin Muammar Gaddafi da kuma kashe shi a shekara ta 2011.

A baya ana sayarwa da ƴan-ta-da ƙayar-baya bindiga ne kawai amma daga baya aka fara ciniki da mayaƙa daga Sudan da kuma maƙotan ƙasashe kamar Chadi.

Amma yanzu mayaƙa suna karbar makaman abokan gaba da aka kashe ko aka kama a birnin Khartoum, daga nan sai su sayarwa dillalan makamai ta hanyar mai shiga tsakani.

Masu buƙatar bindiga su na kiran dillalai su sanar da su irin makamin da suke buƙata, su kuma sai su kaiwa mutum AK-47 har gida sannan su koyarda yadda za a yi amfani da ita.

Shi ko harsashi ana saya rda shi daban-daban ne, ta hanyar alaƙa da dillalai a kasuwar Souq Omdurman dake birnin na Omdurman.

Wani Uba mai shekaru 55, ya bayyana cewar ya sayi AK-47 ne saboda tsaro, bayan yawaitar hare-hare a Khartoum.

Sudan ta faɗa cikin yakin basasa a watan Afrilu, bayan da aka samu saɓani tsakanin babban hafsan sojojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kwamandan RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.

Ɓangarorin biyu sun hamɓarar da gwamnati a watan Oktobar shekara ta 2021, amma rikicin jagoranci ya haifar da rarrabuwar kai tsakaninsu.

Dillalin makaman ya ƙara da cewar banda AK-47, makamin da aka fi buƙata shine ƙaramar bindigar Pistol mai sauƙin ɗauka da kuma amfani.

Magidanta na mallakarta saboda kare kai bayan rushewar gwamnati da ta haifar da rashin ƴan sanda da Alkalai da kuma ma`aikatan gidan kurkuku.

Rikicin na Sudan ya haifar da ƙaruwar laifuka lamarin da ya tilastawa jama`a rufe sana`o`i tare da sallamar ma`aikata abinda ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi.

Duk da matsin rayuwar da al`umma suke fuskanta, da dama daga cikin magidanta sun sayi bindigogi saboda muhimmancin tsaro, musamman yanzu da sace-sace suka yawaita kuma yiwa mata fyaɗe ya zama ruwan dare.

Dillalin makamai ya ce ya rage farashin ƙaramar bindigar pistol daga fan 800,000 na Sudan zuwa fan 200,000 na ƙasar ta sudan.

''Abin da ya sa pistol tsada shine lasisi, amma yanzu ba a buƙatar lasisi kafin mallakarta.''

Yayin da masu AK-47 suke ɓoye ta a gida, su kuwa masu Pistol ɗaukar ta suke yi a jikinsu idan za su gidan mai ko kasuwanni.

Taɓarɓarewar tsaro ta sanya wani mai shekaru 24 wanda ya yi aure shekarun baya kuma ya haifi ɗa mai shekara ɗaya ya gamu da wasu ɓatagari suka ƙwace kuɗadensa kuma suka harbe shi a baya.

Duk da an yi nasarar cire harsashi daga lakarsa bayan tafiyar akalla 200 kafin a samu asibiti, faruwar al`amari ta zama tamkar tunasarwa game da yadda yaƙi ya jefa rayuwar mutane cikin bala`i.