You are here: HomeAfricaBBC2021 05 26Article 1270888

BBC Hausa of Wednesday, 26 May 2021

Source: BBC

Rikicin Isra'ila da Gaza: Nawa Amurka ke kashewa wajen tallafa wa Isra'ila?

Amurka na bai wa Isra'ila baban agaji bangaren kudi da makamai Amurka na bai wa Isra'ila baban agaji bangaren kudi da makamai

Shugaba Joe Biden na fuskantar tambayoyi daga wasu ƴan jam'iyyarsa ta Demokrat kan yawan kuɗin agajin da Amurka ke aika wa Isra'ila.

Sanata Bernie Sanders ya ce dole ne Amurka ta yi zurfin tunani kan yadda ake kashe kuɗin.

Ko nawa Isra'ila ke samu kuma me take yi da shi?

Nawa Amurka ke bayarwa?

A shekarar 2020, Amurka ta bai wa Isra'ila agajin dala biliyan 3.8 - wani ɓangare na wani alƙawari na shekara-shekara na dogon zango da aka ɗauka ƙarƙashin gwamnatin Obama.

Kusan duka agajin da aka bayar a bara na ayyukan soja ne, a cewar Cibiyar Bincike ta Majalisar Dokokin Amurka, CRS.

Yarjejeniyar, wadda tsohon Shugaba Barack Obama ya sa wa hannu a 2016 za ta zo ƙarshe a 2028. Wannan na nufin Isra'ila za ta samu kusan dala biliyan 38 a tallafin ayyukan soji.

An samu ƙari kan yarjejeniyar da tsohon Shugaba George W Bush ya yi da Isra'ila, wadda yawan kuɗin da Amurka za ta bayar cikin shekara goma ya kai dala biliyan 30.

Haka kuma, a shekarar da ta gabata Amurka ta bai wa Isra'ila dala miliyan biyar don amfani da shi wajen sama wa ƴan ci-rani matsugunai a Isra'ilar.

Ƙasar na da wata daɗaɗɗiyar manufa ta amsar Yahudawa daga wasu ƙasashen duniyan a matsayin ƴan ƙasa.

Yaya Isra'ila ta yi amfani da kuɗin na Amurka?

A shekarun da suka wuce, tallafin Amurka ya taimaka wa Isra'ila samar da ɗaya daga cikin rundunonin soji mafi ƙarfi a duniya, inda kudin ya ba su damar sayen kayan aiki mafiya inganci daga Amurka.

Misali, Isar'ila ta sayi jirgin yaƙi na 50 F-35 wanda ake iya amfani da shi wajen kai harin makami mai linzami - kawo yanzu 27 daga cikin jiragen sun isa Isra'ila kuma kowanne ya kai dala miliyan 100.

Bara Isra'ila ta sayi jirgin Boeing KC-46A 'Pegasus' guda takwas kan dala biliyan 2.4. Waɗannan jiragen na iya zuba wa jiragen yaƙi kamar F-35 mai a sararin samaniya.

Cikin dala biliyan 3.8 da aka ba wa Isra'ila a shekarar 2020, an ware dala miliyan 500 don kakkaɓo makamai masu linzami ciki har da inganta na'urar "Iron Dome" mai kakkaɓo rokoki da sauran tsare-tsare kakkaɓo rokoki.

Tun 2011, Amurka ta bayar da tallafin dala biliyan 1.6 ga inganta na'urar Iron Dome.

Haka kuma, Isra'ila ta kashe miliyoyi wajen haɗa kai da Amurka kan inganta fasahar soji kamar gano ramukan ƙarƙashin ƙasa da ake ginawa don shiga Amurka.

Gwamnatin Isra'ila na zuba maƙudan kuɗi wajen sayen kayan yaƙi da horon dakarunta, ta hanyar amfani da tallafin.

Idan aka kwatanta da sauran ƙasashen duniya

Tun yaƙin duniya a biyu, Isra'ila ta kasance kasar da ta fi ko wacce samun tallafin Amurka.

A 2019, shekara ta baya-bayan nan da aka wallafa cikakkun alkaluma, Isra'ila ce ƙasa ta biyu da ta fi ko wacce samun tallafin ƙasashen waje da Amurka ke bayar wa baya ga Afghanistan a cewar hukumar USAID.

Mafi yawan kuɗin da aka bai wa Afghanistan din, an yi amfani da shi ne wajen tallafa wa ƙoƙarin Rundunar Sojin Amurka na samar da zaman lafiya a ƙasar, wadda yaƙi ya ɗaiɗaita tun da Amurkar ta tura sojojinta a 2001.

Amma yanzu da ake shirin janye dakarun na Amurka daga Afghanistan nan da watan Satumban wannan shekarar, kusan dala miliyan 370 ne kawai aka buƙata a shekarar 2021.

Isra'ila na karɓar kuɗi fiye da ko wace ƙasa a Gabas ta Tsakiya.

Masar da Jordan su ma suna cikin manyan masu karɓar kuɗin tallafin Amurka. Ƙasashen biyu duk suna da yarjejeniyoyinsu na zaman lafiya da Isra'ila tunda duk sun taɓa yaƙi da ita.

Ko wacce daga cikinsu ta samu kusan dala biliyan 1.5 na tallafin Amurka a 2019.

A wani ɓangaren kuma, Shugaba Biden ya dawo da bayar da wasu kuɗi (dala miliyan 235) fa hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ke taimaka wa ƴan gudun hijirar Falasɗinu. Gwamnatin Trump ta rage yawan wannan tallafin a 2018.

Meya sa Amurka ke ba Isra'ila tallafi da yawa?

Akwai dalilai da dama da Amurka ke bai wai Isra'ila tallafin kuɗi, ciki har da alkawarin da ke tsakanin ƙasashen biyu na tarihi wanda Amurka ta yi a 1948.

Baya ga haka, Amurka na ganin Isra'ila a matsayin ƙawarta mai muhimmanci a Gabas ta Tsakiya - inda suke da burace-burace masu kama dangane da dimokuraɗiyya.

Cibiyar Bincike ta Majalisar Dokokin Amurka ta ce: "Tallafin da Amurka ke ba kasashen waje ya zama wani ginshiki na ƙarfafa ƙawance.

"Jami'an gwamnatin Amurka da ƴan majalisa sun daɗe da yi wa Isra'ila kallon ƙawa mai muhimmanci a yankin."

Hukumar gwamnatin Amurka da ke kula da tallafin da ƙasar ke bai wa ƙasashen waje ta ce: "Tallafin Amurka na taimakawa wajen tabbatar da cewa Isra'ila na ci gaba da kula da ingancin rundunarta kan barazanar da ka iya tasowa daga yankin."

Tabbatar da cewa Isra'ila za ta iya kare kanta daga duk wata barazana a yankin shi ne babban jigon manufar kasashen waje ta Amurka ga shugabannin Democrat da na Republican tsawon shekaru.

A 2020, jam'iyyar Democrat ta bayyana cewa za ta bai wa Isra'ila "ƙwaƙƙwaran tallafi" amma wasu ƴan jam'iyyar a yanzu suna tantama kan tallafin na Amurka.

Sanata Sanders da sauran ƴan Democrat suna ƙoƙarin ganin an dakatar da shirin sayar wa Isra'ila makamai na dala miliyan 735.