You are here: HomeAfricaBBC2023 01 17Article 1696979

BBC Hausa of Tuesday, 17 January 2023

Source: BBC

Real za ta yi wasa biyar kafin ta je Club World Cup a Morocco

Karim Benzema Karim Benzema

Real Madrid za ta buga Club World Cup a birnin Morocco ranar 8 ga watan Fabrairu a Morocco, kafin nan tana da wasa biyar masu zafi a gabanta.

A ranar Alhamis za ta kara da Villareal a wasan kungiyoyi 16 a Copa del Rey a filin Estadio de la Ceramica.

Wasa na biyu kuwa za ta yi a waje ranar Lahadi da Athletic karawar mako na 18 a gasar La Liga a filin wasa na San Mames.

Idan Real Madrid ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a Copa del Rey, za ta buga wasan ranar 25 ko 26 ga watan Janairu.

Real za ta karkare watan Janairu da fafatawa a gida da Real Sociedad ranar 29 ga watan nan.

Kwana hudu tsakani Real ta karbi bakuncin Valencia ranar 2 ga watan Fabrairu a kwantan La Liga, bayan da suka buga Spanish Super Cup a Saudi Arania.

Wasa na karshe da Real za ta yi kafin ta je Morocco shi ne da Mallorca ranar 5 ko kuma 6 ga watan Fabrairu.

Wasa biyar da ke gaban Real Madrid:

Villarreal da Real Madrid Copa del Rey: Alhamis 19 ga Janairu.

Athletic da Real Madrid LaLiga, wasan mako na 18): Lahadi 22 ga Janairu.

Real Madrid da Real Sociedad LaLiga, wasan mako na 19): Lahadi 29 ga Janairu

Real da Valencia LaLiga, kwantan wasan mako 17): Alhamis 2 ga Fabrairu.

Mallorca da Real Madrid LaLiga, wasan mako na 20): 4-5 Fabrairu