You are here: HomeAfricaBBC2023 08 07Article 1820216

BBC Hausa of Monday, 7 August 2023

Source: BBC

Real Sociedad na tattaunawa da Van de Beek

Donny van de Beek Donny van de Beek

Dan wasan Manchester United Donny van de Beek yana tattaunawa da Real Sociedad game da barin Old Trafford.

United ta biya fan miliyan 35 kan Van de Beek shekara uku da suka wuce.

Sai dai dan kasar Holland din ya gaza taka rawar gani a Premier League kuma zuwan tsohon kocin Ajax Erik ten Hag ma bai sauya lamarin ba.

Van de Beek ya fara wasan share fage na karshe da Athletic Bilbao a Dublin amma an maye gurbinsa a hutun rabin lokaci.

Dan wasan mai shekara 26 yana daya daga cikin ’yan wasan da United ke bukatar ta sallama domin samar da karin kudade ga Ten Hag don kara wa kungiyarsa ƙarfi a bazara.

Mai tsaron gida Dean Henderson zai iya komawa Nottingham Forest amma yanayinsa na da sarkakiya saboda raunin cinyar da ya ji a watan Janairu wanda ya hana shi buga duk wani wasa a wasannin share fage.

An shaida wa mai tsaron baya Eric Bailly cewa zai iya neman sabon kulob kuma ba ya cikin tsarin Ten Hag a Old Trafford.

A halin yanzu, Fulham na ci gaba da sha'awar dan wasan tsakiya na Brazil Fred amma ya zuwa yanzu ba ta gabatar da wani tabbataccen tayi kan dan wasan ba.