You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853996

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Real Madrid ta koma ta biyu bayan doke Las Palmas

Yan wasan Real Madrid Yan wasan Real Madrid

Real Madrid ta koma cin wasa bayan lallasa Las Palmas 2-0 a filin wasanta na Santiago Bernabeu cikin sauƙi ranar Laraba.

Rashin nasara da ta yi a hannun abokiyar hamayya Atletico Madrid ya sa aka kawo ƙarshen wasan La Liga biyar da ta buga ba tare da an ci ta ba a ranar Lahadi.

Amma ƙwallayen da Brahim Diaz da Joselu suka jefa a ragar Palmas na nufin Real ta koma ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, maki ɗaya tsakaninta da Girona da ke saman teburin da kuma maki ɗaya da ta ba wa Barcelona a mataki na uku.

Tawagar ta Carlo Ancelotti ce ta mamaye fallen farko na wasan, amma sai da aka ƙara lokaci kafin tafiya hutu sannan Brahim ya jefa ƙwallon farko a raga.

Kazalika, ƙwallon da Joselu ya murza da kansa ce a minti na 54 ta bai wa Real cikakkiyar nasara.

Tauraron ɗan wasa Jude Bellingham bai buga wasan ba, inda Ancelotti ya sauya mutum biyar daga tawagar tasa da ta sha kashi a hannun Atletico.