You are here: HomeAfricaBBC2023 09 15Article 1844405

BBC Hausa of Friday, 15 September 2023

Source: BBC

Real Madrid ta fara shirin fuskantar Real Sociedad a La Liga

Hoton alama Hoton alama

Bayan kammala wasanin kasa da kasa 'yan wasa sun fara komawa kungiyoyinsu tun daga ranar Laraba, inda Real ke shirin fuskantar Sociedad a karshen mako

Tuni Real Madrid ta fara atisayen tunkarar wasan mako na biyar da za ta yi da Sociedad a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Cikin 'yan wasa da Carlo Ancelotti ya yi atisaye da su har da na matasan kungiyar wato Castilla, inda suka fara da zagaye fili.

Daga nan suka koma wasa da tamaula har da bani in baka da raba kwallo a dan karamin fili.

Haka kuma Ceballos da Mendy sun yi atisaye tare da rukunin 'yan wasa.

Shi kuwa Vini Jr. da Arda Guler sun motsa jiki a rufaffen daki a kokarin da suke na murmurewa, bayan jinya.

Shima Tchouameni, wanda ke murmurewa ya yi atisayen a rufaffen dakin.

Sakamakon wasannin da suka kara a 2022/2023

Ranar Talata 2 ga watan Mayun 2023


  • Sociedad 2 - 0 Real Madrid

Ranar Lahadi 29 g watan Janairu 2023


  • Real Madrid 0 - 0 Sociedad

Real Madrid ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 12, bayan lashe wasa hudu a jere a bana, Girona ta biyu da maki 10, Barcelona maki 10 ne da ita.

Kungiyar Atletico Madrid ce ta hudu mai maki bakwai, wadda za ta ziyarci Valencia ranar Asabar.

Ranar Juma'a 15 ga watan Satumba


  • Rayo Vallecano da Deportivo Alaves

Ranar Asabar 16 ga watan Satumba


  • Athletic Bilbao da Cadiz
  • Valencia da Atletico Madrid
  • Celta de Vigo da Real Mallorca
  • FC Barcelona da Real Betis

Ranar Lahadi 17 ga watan Satumba


  • Getafe da Osasuna
  • Villarreal da UD Almeria
  • Sevilla da Las Palmas
  • Real Madrid da Real Sociedad

Ranar Litinin 18 ga watan Satumba


  • Granada da Girona