You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824782

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Real Madrid ta dauki aron golan Chelsea Arrizabalaga

Kepa Arrizabalaga Kepa Arrizabalaga

Real Madrid ta kammala daukar aron golan Chelsea, Kepa Arrizabalaga zuwa karshen kakar bana.

Mai shekara 28 zai maye gurbin Thibaut Courtois, wanda ya ji rrauni ranar Alhamis, zai kuma yi jinya mai tsawo.

Kepa ya yi wasa 163 a Chelsea tun bayan da ya koma Stamford Bridge daga Athletic Bilbao kan fam miliyan 71 a Agustan 2018 a matakin mai tsaron raga mafi tsada.

Chelsea ta yi amfani da Sanchez, wanda ta dauka kan fam miliyan 25 a karawar Premier League da ta tashi 1-1 da Liverpool ranar Asabar a Stamford Bridge.

Chelsea ta sayar da mai tsaron ragar tawagar Senegal, Edouard Mendy ga Al-Hilal ta Saudi Arabia a bana.

Barin Chelsea da Kepa ya yi, yanzu saura Marcus Bettinelli, mai shekara 31 da mai shekara 20 Lucas Bergstrom da mai shekara 19, Eddie Beach masu tsaron raga a kungiyar Stamford Bridge.

Real Madrid ta fara cin Athletico Bilbao 2-0 a wasan farko a La Liga na bana ranar Asabar.

Dan kwallon da ta dauka kan fara kakar nan Jude Bellingham, kan fam miliyan 88.5 daga Borussia Dortmund, shima ya ci kwallo a karawar.