You are here: HomeAfricaBBC2023 02 19Article 1717367

BBC Hausa of Sunday, 19 February 2023

Source: BBC

Real Madrid ta ci wasa na 100 a La Liga da Courtois a raga

Thibaut Courtois Thibaut Courtois

Real madrid ta je ta doke Osasuna 2-0 ranar Asabar a wasan mako na 22 a gasar La Liga.

Thibaut Courtois ne ya tsare ragar Real, wasa na 151 da ya yi a La Liga, karo na 100 da kungiyar Santiago Bernabeu ta ci wasa da golan a cikin raga.

Mai ttsaron ragar tawagar Belgium, wanda ya yi wasa na 151 a La Liga ranar Asabar, yana kaka ta biyar a Real Madrid.

Kakar da Real ta ci wasannin La Liga da yawa tare da Courtois ita ce ta 2021/22 da ta ci 26 da kuma 2020/21 da ta yi nasara a wasa 25.

A wasannin bana, Real Madrid ta yi nasara 12 daga 16 a gasar La Liga da take yi ta bana, wadda take ta biyu a teburi, biye da Barcelona ta daya.

Sau biyu Courtois ya lashe La Liga, wanda a kakar 2019/20 ya karbi kyautar Zamora a matakin wanda yafi taka rawar gani a kakar.

A kakar biyar da Courtois yake a Santiago Bernabeu ya ci Champions League da Club World Cups biyu da European Super Cup da Spanish Super Cups biyu.