You are here: HomeAfricaBBC2023 07 06Article 1799336

BBC Hausa of Thursday, 6 July 2023

Source: BBC

Real Madrid ta ɗauki Arda Guler daga Fenerbahce

Arda Guler Arda Guler

Real Madrid ta kammala ɗaukar matashin ɗan wasan Turkiyya ɗan shekara 18 Arda Guler daga Fenerbache.

Dan wasan da ake kira Messin Turkiyya ya sanya hannu kan kwantaragin shekara shida a Bernabeu inda zai haɗu da ɗan wasan Ingila Jude Bellingham.

A bara Guler ya ci kwallo huɗu ya kuma bayar da huɗu an ci, kuma shi ne ya zama ɗan wasan da ya fi ko wanne ƙoƙari a wasan ƙarshe na Kofin Turkiyya.

A watan jiya ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa ci wa Turkiyya kwallo a tarihi.

Guler ya fara buga wa Fenerbache wasa ne lokacin yana da shekara 16, ya kuma bayar da kwallo an ci a wasan farko da ya buga a Super Lig kuma daga baya ƙungiyar ta ba shi lamba 10 a bara.

Da wannan ɗaukar da Real Madrid ta yi masa, yanzu ta buge ƙungiyoyin Premier uku da suka haɗa da Manchester United da Arsenal da kuma Newcastle, baya ga Bayern Munich da Paris St-Germain da suma suka nuna sha'awarsu.

Real Madrid ba ta bayyana nawa ta sayi ɗan kwallon ba, amma rahotanni na cewa yuro miliyan 20 aka saye shi.

Guler shi ne na baya-bayan nan da ƙungiyar ta ɗauka na matasan 'yan kwallo irinsu Bellingham da Vinicius Jr da Rodrygo da Aurelien Tchouameni da kuma Eduardo Camavinga.