You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1854011

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Real Madrid na kwaɗayin De Zerbi, Saudiyya za ta shiga farautar Osimhen

Kocin Brighton Roberto de Zerbi Kocin Brighton Roberto de Zerbi

Kocin Brighton Roberto de Zerbi da Xabi Alonso na Bayer Leverkusen na cikin mutanen da ake tunanin za su iya maye gurbin Carlo Ancelotti idan ya bar Real Madrid yayinda kwantiraginsa ke gab da karewa a ƙarshen kaka. (Cadena Ser - in Spanish)

Ana ganin zai yi wahala a samu daidaituwa tsakanin Kocin Manchester United Erik ten Hag da ɗan wasan gefe Jadan Sancho mai shekara 23. (The i)

Ƙungiyoyin Saudiyya za su jagorancin farautar ɗan wasan Najeriya da ke taka leda a Napoli, Victor Osimhen. Saudiyya na fatan ta sha gaban Real Madrid da Chelsea da duk ke kwaɗayin sayen matashin mai shekara 24 a Janairu.(Mail)

Sevilla na bibbiyar ɗan wasan tsakiya Hannibal Mejbri, mai shekara 20, amma Manchester United na shirin gabatar da sabon tayi kan ɗan wasan na Tunisia saboda ya ci gaba da zama a Old Trafford. (Fabrizio Romano)

Manchester United na kuma shirin shiga tattaunawa kan yiwuwar sabunta kwantiragin Erik ten Hag da sabuwar yarjejeniya. (90Min)

Chelsea ta shiga farautar ɗan wasan baya, inda take harin ɗan wasan Inter Milan mai shekara 25 Federico Dimarco na Italiya da kuma Theo Hernandez da ke taka leda a AC Milan. (Calciomercato - in Italian)

Sheffield United ta tattauna da tsohon kociyanta Chris Wilder kan yiwuwar maye gurbin Paul Heckingbottom.(Football Insider)

Roma na duba yiwuwar saye ɗan wasan Tottenham mai shekara 29, Eric Dier a cikin watan Janairu. (Calciomercato - in Italian)

Makomar tattalin arzikin Everton za ta shiga wani yanayi idan aka gaza cimma daidaituwa da kamfanin 777 na Amurka.(Guardian)

777 na da kwarin gwiwar cimma duk wasu ƙa'ida na shugabannin kulob din na firimiya, kuma ya soma tattaunawa da magoya-bayan Everton saboda a kwantar musu da hankali.. (The i)

Newcastle ta kawo karshen yarjejeniyar rigarsu da Castore kan damuwar da ake nunawa kan ingancinta. (Telegraph- subscription required)