You are here: HomeAfricaBBC2023 09 21Article 1848659

BBC Hausa of Thursday, 21 September 2023

Source: BBC

Rashin nasarar da United ta yi kuskurena ne - Onana

Andre Onana Andre Onana

Golan Manchester United Andre Onana ya ce laifinsa ne da United ta yi rashin nasara a wasanta na gasar zakarun Turai da Bayern Munich.

A wani gagarumin wasa da aka buga a Jamus, kuskuren Onana ya bai wa Bayern damar cin kwallon farko, a inda suka ƙara ta biyu cikin kanknin lokaci.

United ta kasa farfaɗowa daga nan har aka tashi wasan inda Batern ta yi nasara da ci 4-3.

Onana ya koma United ne a bazara kan fam miliyan 47.2 bayan ya taimaka wa Inter Milan ta kai wasan ƙarshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta bara.

Sai dai kuma ɗan wasan na Kamaru ya sha fama a wasu lokutan, inda aka zura masa kwallaye 14 a wasanni shida da ya buga a dukkanin gasa.

Yanzu United ta sha kashi a wasanni huɗu daga cikin shidan da ta buga a kakar wasa ta bana kuma an doke ta a wasaninta uku na ƙarshe.