You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806353

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Rashford zai ci gaba da taka leda a Man United

Marcus Rashford tare da Erik Ten Hag Marcus Rashford tare da Erik Ten Hag

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford yana daf da kulla yarjejeniya ci gaba da taka leda a kungiyar.

Mai shekaru 25 ya shafe watanni yana tattaunawa kan tsawaita kwantiraginsa, bayan da yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kaka mai zuwa.

Kungiyoyi da dama sun nuna sha'awar son daukar dan wasan gaba na Ingila, amma zabin da ya fi so shi ne ya ci gaba da zama a Old Trafford.

Kocin kungiyar Erik ten Hag yana son ci gaba da aiki tare da Rashford, an fahimci cewa an kusa kammala kulla yarjejeniyar ta tsawon shekaru biyar.

Kenan zai ci gaba da wasa a kungiyar har zuwa lokacin da zai kai shekara 30 da haihuwa.