You are here: HomeAfricaBBC2023 02 19Article 1717355

BBC Hausa of Sunday, 19 February 2023

Source: BBC

Rashford ya zama na farko da ya ci kwallo a wasa bakwai a jere a Old Trafford

Marcus Rashford Marcus Rashford

Manchester United ta doke Leicester City 3-0 a wasan mako na 24 a gasar Premier da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.

United ta fara cin kwallo ta hannun Marcus Rashford a minti 25 da fata tamaula, sannan ya kara na biyu da aka koma zagaye na biyu.

Jadon Sancho ne ya ci wa United na uku, wadda ta hada maki ukun da take bukata a fafatawar.

Rashford ya zama na farko da ya ci kwallo a wasa bakwai a jere a Premier League a Old Trafford, tun bayan bajintar Wayne Rooney a 2010.

Haka kuma dan wasan tawagar Ingiila ya ci kwallo 17 a Old Trafford a bana a dukkan fafatawa.

Ya kafa wannan bajintar tunbayan kwazon Rooney a kakar 2011-12, wanda ya zura 19 a raga.

Da wannan sakamakon United tana ta uku a kan teburin Premier da maki 49 da tazarar uku tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Ranar Alhamis United za ta kece raini a wasa na biyu da Barcelona a Old Trafford, sannan ta buga karawar karshe da Newcastle United a Wembley ranar Lahadi.

United ta je ta tashi 2-2 da Barcelona a zagayen farko a neman gurbin shiga 'yan 16 da za su ci gaba da karawar Europa League a bana.