You are here: HomeAfricaBBC2023 04 12Article 1747919

BBC Hausa of Wednesday, 12 April 2023

Source: BBC

Rashford ba zai yi wa United wasu wasannin ba

Marcus Rashford Marcus Rashford

Marcus Rashford ba zai buga wa Manchester United wasu wasannin ba, sakamakon jinya da zai yi.

Mai shekara 25 dan kwallon tawagar Ingila ya ji rauni ranar Asabar a karawar da United ta ci Everton a wasan Premier League.

United ba ta fayyace kwanakin da zai yi jinya ba, illa ta ce zai murmure ya buga mata tamaula kafin karshen kakar nan.

Rashford mai kwallo 28 a bana ya buga wa United dukkan karawar lik a 2022/23.

United za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan farko a quarter final ranar Alhamis a Europa League a Old Trafford.

An canja da wasan a minti na 80 ranar Asabar, bayan da United ta doke Everton 2-0 a Old Trafford, yana fita daga fili ya wuce dakin hutun 'yan wasa.

Za a ci gaba da auna koshin lafiyar dan kwallon a lokacin da yake jinya, wanda ake fatan zai ci gaba da taka leda kafin a karkare kakar nan.