You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853927

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Raphinha zai yi jinyar wata ɗaya

Raphinha Raphinha

Ɗan kwallon Barcelona, Raphinha zai yi jinYar wata Ɗaya sakamakon raunin da ya ji, in ji wani rahoto daga Sifaniya.

Kungiyar ta sanar da cewa ɗan wasan tawagar Brazil ya ji rauni ranar Juma'a a gasar La Liga da ta ci Sevilla, wanda hakan ya mayar da Barca matakin farko a teburi a ranar.

Raphinha, wanda ya buga karawar daga matakin ɗan tsakiya, an sauya shi da Fermin Lopez tun kan hutu, bayan raunin da ya ji.

Ɗan kwallon ba zai buga wasan Champions League da za ta ziyarci Porto ba ranar Laraba da kuma wanda za ta ziyarci Granada a La Liga ranar 8 ga watan Oktoba.

Haka kuma zai ci gaba da jinya har bayan wasan hamayya na El Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid ranar 28 ga watan Oktoba.

Mai shekara 26 an yi masa jan kati a wasan farko a karawa da Getafe ya kuma samu damar shiga wasa ne a lokacin, bayan da matasa Lamine Yamal da kuma Ferran Torres ke taka rawar gani.

'Yan wasan Barcelona da ke jinya a yanzu haka sun haɗa da Pedri da kuma Frenkie de Jong.