You are here: HomeAfricaBBC2023 03 09Article 1728038

BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023

Source: BBC

Ranar Mata ta Duniya: Matan Instanbul sun yi burus da haramcin yin zanga-zanga

Hoton alama Hoton alama

Dubban matan Turkiyya sun yi watsi da haramcin yin zanga-zanga a ranar mata ta duniya inda suka yi tattaki a birnin Instanbul saboda abin da suka kira "Tattakin dare kan rajin kare ƴancin mata."

Ƴan sanda sun hana su isa dandalin Taksim da ke tsakiyar birnin amma sun ƙyale su, su ci gaba da tattakin na wani lokaci duk da cewa daga baya, an yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa su.

Ƴan sanda sun tsare mutane da dama yayin gangamin.

Babbar Jam'iyyar hamayya ta Republican People's Party ta gudanar da bikin ranar tare da fitar da wata sanarwa kan irin aƙubar da ta ce ana yi wa mata a ƙasar.

A sanarwar ta fitar da wani rahoto wanda a ciki ta ce maza sun kashe sama da mata 600 a Turkiyya tun daga 2021 inda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya janye ƙasar daga yarjejeniyar Instanbul.

Yarjejeniyar na son yaƙi da cin zarafin da mata ke fuskanta a gida.

Mun sanya muku wasu daga cikin hotunan yadda zanga-zangar matan ta kasance.