BBC Hausa of Friday, 14 July 2023
Source: BBC
Bayan da Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu, ta neman Naira biliyan 500 don rage radadin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi, yanzu haka ana ci gaba da bayyana ra'ayoyi masu cin karo da juna kan yadda tallafin zai shafi jama'a.
Ita dai gwamnatin shugaban kasar ta tsara cewa za ta rika biyan kimanin mutum miliyan 12 tallafin Naira dubu takwas a duk wata har tsawon watanni shida, domin ganin kudin ya zagaya, arziki ya karu a tsakanin jama'a.
Sai dai wasu daga cikin 'yan jam'iyyarsa ta APC na ganin ko a gwamnatin baya ta tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari an gwada irin wannan, amma bai yi wani tasiri ba.
Injiniya Sani Bala Tsanyawa, wani dan majalisar wakilai daga jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa sun amince da bukatar ne saboda wannan na daya daga cikin bukatun shugaban na farko, amma ba ya ji hakan zai yi wani tasiri.
A cewarsa: ''Abun a yaba ne farawar da aka yi, amma ko cewa aka yi mutum na daukar albashi ka kara masa Naira dubu takwas, babu wani abu da za ta masa, ballantana kuma mutumin da ko yaushe yana gida babu abun da yake yi.
''Wannan adadi ko kashi goma na 'yan Najeriya bai kai ba, mutum miliyan goma sha biyu cikin sama da talakawa miliyan dari da hamsin ai ka ga babu abin da aka yi'' in ji shi.
Ya nanata cewa akwai bukatar a ce wannan adadi ya fi haka, duba da cewa lamarin ya shafi kowa da kowa ne.