You are here: HomeAfricaBBC2021 04 10Article 1228627

BBC Hausa of Saturday, 10 April 2021

Source: BBC

Rabon da Messi ya ci Real tun Ronaldo da ya koma Juve

Lionel Messi, dan wasan Barcelona Lionel Messi, dan wasan Barcelona

Ranar Asabar za a yi karan batta a wasan hamayya wato El Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona da za su fafata a karawar mako na 30 a gasar La Liga.

Kawo yanzu kyaftin din Barcelona, Lionel Messi ya ci kwallo 23 a gasar La Liga, zai kuma so ya kara cin wasu a ragar Real Madrid a wasan da za su buga a Alfredo Di Stefano.

Dan wasan tawagar Argentina bai samu damar zura kwallo ba a ragar Real Madrid a wasan farko da suka buga a bana, inda Real ta ci 3-1 a cikin watan Oktoba a Camp Nou.

Rabon da Messi ya ci Real Madrid tun 2018 a kakar da Cristiano Ronaldo ya koma taka leda a Juventus, kuma wasa shida baya kyaftin din bai ko bayar da kwallo aka zura a ragar Real ba.

Wasan karshe da ya ci Real shi ne karawar La Liga fafatawar mako na 36 a shekarar 2017/18 da suka tashi 2-2 a Camp Nou.

Messi wanda a baya ke cin Real abokiyar hamayya, ya zura 21 a raga a fafatawa 27 - sai dai yanzu ya yi kasa inda ya ci biyar a wasa 17 baya da suka hadu.

Barcelona ce ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Atletico ta daya, Real ce ta uku da tazarar maki biyu tsakaninta da kungiyar Camp Nou.

'Yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga:

  • Lionel Messi, FC Barcelona - 23


  • Gerard Moreno, Villarreal - 19


  • Luis Suarez, Atletico Madrid - 19


  • Karim Benzema, Real Madrid - 18


  • Youseff En-Nesyri, Sevilla - 15


  • Rafa Mir, Huesca - 12


  • Alexander Isak, Real Sociedad - 12


  • Jose Luis Morales, Levante - 11


  • Roger Marti, Levante - 11


  • Mikel Oyarzabal, Real Sociedad - 10


  • Iago Aspas, Celta de Vigo - 10