You are here: HomeAfricaBBC2023 02 14Article 1714355

BBC Hausa of Tuesday, 14 February 2023

Source: BBC

Qatar ta aika da gidajen tafi-da-gidanka 10,000 zuwa Turkiyya da Syria

Hotunan dakunan Hotunan dakunan

Ƙasar Qatar ta aika da gidaje irin na 'tafi-da-gidanka' wadanda 'yan kallon gasar kwallon kafa ta duniya da aka yi a kasar zuwa yankunan da girgizar kasa ta daidaita a Turkiyya da Syria.

Wannan na matsayin tallafi ga mutanen kasashen biyu da suka rasa muhallansu a sanadin iftila'in da ya afka wa yankin.

Gidajen irin na tafi da gidanka ne, wato a kan hada su ne a wuraren da ake bukatarsu, kuma daga baya ana iya kwance su a kai su duk wurin da ake bukata a kuma hada su a can.

Wani jirgin ruwa dauke da gidaje 350 - rukunin farko na gidajen - ya bar Qatar zuwa Turkiyya a ranar Lahadi.

Asusun raya kasar Qatar ya yi alkawarin aika wa kasashen biyu irin wadannan gidajen guda 10,000.

Wata sanarwa da asusun ya wallafa a shafinsa na Tiwita na cewa: "A dalilin bukatun gaggawa da ake da ita a Turkiyya da Syria, mun yanke shawarar aika wa da wadannan gidajen na tafi da gidanka zuwa yankin, domin samar da tallafin da aka fi bukata da kuma taimaka wa al'umomin Turkiyya da Syria."

Kawo yanzu dai akwai alkaluman mutum fiye da 36,000 da suka halaka a sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 7.8 da ta afka wa yankin kudu maso gabashin Turkiyya da na arewa maso gabashin Syria mai makwabtaka.

Tun farko dama Qatar ta yi niyyar raba wa kasashe masu bukata wasu daga cikin kayayyakin da aka yi amani da su yayin gasar cin kofin duniyar wanda aka yi a watan Nuwambar bara.

Wadannan gidajen na tafi da gidanka na cikin rukunin gine-ginen da za a rabar, baya ga wasu filayen wasa na musaman da aka gina da niyyar kwance su kacokan domin a yi wa wasu kasashen duniya kyautar su.

Yayin gasar cin kofin duniyar, 'yan kallo sun rika biyan dala 200 a matsayin kudin hayan kowane gida a kowane kwana guda, a wannan gasar da aka yi tsakanin watan Nuwamba zuwa na Disambar 2022 a birnin Doha.