You are here: HomeAfricaBBC2023 09 12Article 1842980

BBC Hausa of Tuesday, 12 September 2023

Source: BBC

Putin da Kim: Abokai a lokacin neman makamai

Vladimir Putin da Kim Jong Un Vladimir Putin da Kim Jong Un

Vladimir Putin da Kim Jong Un tasu ta zo ɗaya a abubuwa da dama.

Dukkan su ba su fitowa waje sosai. Shugaban Rasha bai bar ƙasar ba a wannan shekarar baki ɗaya. Shi kuma Kim shekararsa huɗu bai bai ƙasarsa ba.

Daga Rasha har Koriya ta Arewa ana zargin su da zama ƙasashe "masu yin abin da suka ga dama".

Dukkansu ƙasashen duniya sun ƙaƙaba musu takunkumai.

Duka gwamnatocin na adawa da "kaka-gidan" da Amurka ta yi.

A mafi yawan lokaci ƙaramin abokin gaba kan haɗa kan shugabannin wuri ɗaya.

A wajen Putin da Kim. Suna da alaƙa mai ƙarfi, ko da ba ta dindindin ba, amma dai yanayin siyasa ya haɗa kansu a 2023.

Shaƙuwa da juna? gaskiya ba haka ba ne. Ba kamar tsohon shugaban Amurka ba Donald Trump wanda a baya ya ayyana Kim Jong Un a matsayin wanda suka "shaƙu", shugabannin Rasha da Koriya ba su fiye nuna damuwa da juna ba a bainar jama'a.

Amma da alama su biyun za su amfana da wannan alaƙar ta su.

Fuskar ƙaruwa

To da me Kremilin za ta ƙaru?

Da farko dai, Koriya ta Arewa na da gagarumar harkar kere-kere a fannin tsaro inda take da kwarewa mai ɗumbin yawa na sarrafa kayayyakin aikin soja, yayin da yaƙin Rasha ke yi a Ukraine ke jan ƙafa, Pyongyang za ta iya zama hanyar samun makamai a wajen Moscow.

Tuni dai Amurka ta fara zargin cewa Rasha ta ɗana tarkon hakan. Amurka ta sha iƙirarin cewa tattaunawar makamai tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa ta ƙara faɗaɗa, inda ita Rasha ke keman samun makamai da makaman atilare da ake harbawa.

Jami'an Rasha dai ba su tabbatar da hakan ba. Amma alamu da dama sun ba da haske kan cewa Rasha da Koriya ta Arewa na son ƙrfafa haɗin kan ayyukan sojinsu.

A watan Yuli ne Sergei Shoigu ministan harkokin tsaron Rasha ya kai ziyara Koriya ta Arewa, inda ya zama jami'i na farko da ya kai irin wannan ziyara tun bayan karyewar tarayyar sobiyet, lokacin da halarci taron cika shekara 70 da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Koriya.

Kim ya shirya wani faretin soji domin ya nuna masa makaman da suke da shi. Ministan tsaron ya kuma ba da haske kan wani atisayen soji tsakanin su.

"Idan har za su iya neman makamai daga Koriya ta Arewa, ɗaya daga cikin ƙasashe matalauta da rashin ci gaba a duniya - wadda aka mayar saniyar ware - a danina wannan abin kunya ne ga ƙarairayin da Rasha ke yi na cewa tana da ƙarfin iko" in ji tsohon ministan tsaro na Rasha Andrei Kozyrev. Wanda ya bayyana wannan ra'ayi a wani bidiyo daga Amurka inda yake zaune yanzu.

"Ƙasar da ta-kai-ta-kawo ba za ta je wajen Koriya ta Arewa neman ƙawance ba ko kuma sayan makaman soji."

Kith da Kim

Amma yiyuwar samun niyyar sauya dokokin duniya. Da yadda ya mamayi Ukraine, Putin ya nuna wata alama kan yunƙurinsa na juya dokokin duniya kamar yadda yake yi wa Rasha. Sai dai haɗin kan sojin da Koriya ta Arewa ya nuna wata alama kan haka.

Yarjejeniyar makamai tsakanin Moscow da Pyongyang za ta ƙara tabbatar da haka. Har sai a baya-bayan nan da Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya sanya wa Rasha ya sanyaya gwiwowinta kan sayan makamin nukiliya da za ta saya daga Koriya ta Arewa. Ban da wasu takunkuman da aka sanya mata na kasuwanci.

"Gwamnatin Moscow ta sanya hannu kan ƙudurorin Kwamtin tsaro na MDD," kamar yadda jaridar Moskovsky Komsomolets ta Rasha ta tunawa masu karatu a makon jiya. Bamma ta ƙara da cewa hakan ba wani abu ba ne, "domin akan iya janye sa hannun nata".

Kamar yadda jaridar ta ambato shuagaban majalisar harkokin wajen da tsara manufofin tsaro na ƙasar Fyodor Lukyanov yake faɗa.

"Wata tambaya da take yawo a zukatan mutane na dogon lokaci ita ce, Me ya sa mu Rasha muke bin waɗan nan takunkumai da aka sa mana? tsarin alaƙar ƙasashen wajen ya tattaru a hannun kasa ɗaya tilo.

"Ba shakka takunkumin MDD na da halasci. Mawuyacin abu ne ka kore shi. Mun zaɓe su. Amma yanayi ya sauya. Saboda me ba za mu jenye ƙuri'unmu ba?"

Za su iya zama tare har abada?

Mene ne kuma abin da Koriya ta Arewa za ta so ta samu daga Rasha?

Babu makawa cewa za su buƙaci samun tallafin jin ƙai domin shawo kan matsalar ƙarancin abinci da Koriya ta arewar ke fama da shi.

Haka nan akwai raɗe-raɗin da ke cewa Koriya ta arewa na neman samun fasahar sarrafa tauraron ɗan'adam da makaman soji, ciki har da na jiragen da ke tafiya ƙarƙashin ruwa waɗanda ke amfani da ƙrfin nukiliya.

Sama da shekara guda bayan yaƙin da ta tsunduma kanta, wanda ya zame mata alaƙaƙai, Rasha za ta so ta so ta sake haɓɓaka rumbunan makamanta.

Za ta so cin gajiyar dangantakarta da Koriya ta arewa wajen cimma haka.

Sai dai hakan ba yana nufin cewa makaman Rasha za su ƙare ba ne idan babu Koriya ta arewa.

Tsohon ministan waje, Andrei Kozyrev ya ce "Putin ba a matse yake ba."

"Zai iya ci gaba da tafiyar da lamurransa na tsawon lokaci. A kowace rana yana koyon darasi kan yadda zai kauce wa illar takunkumai, da yadda zai haɗa kai da China, da Koriya ta arewa da wasu ƙasashen Afirka.

Wannan ba wani lamari ne da zai daɗe nan gaba ba, to amma zaɓi ne mai kyau a wannan lokaci da kuma ƙila wasu shekaru masu zuwa."