You are here: HomeAfricaBBC2021 04 10Article 1228639

BBC Hausa of Saturday, 10 April 2021

Source: BBC

Prince Philip: Yarima dan zamani

Yariman Edinburgh ya kasance mai tafiya da zamani Yariman Edinburgh ya kasance mai tafiya da zamani

Yariman Edinburgh ya kasance mai tafiya da zamani, wanda ya gamsu da irin rawar da kimiyya da fasaha kan taka wajen inganta rayuwa

Ra'ayinsa ya yi daidai da na Yarima Albert wanda sha'awarsa game da abubuwan da juyin juyaya halin masana'antu ya kawo, ya sa shi kirkirar Babban Baje-koli, wanda ba a taba yin irinsa ba, a 1851.

Yarima Philip ya kasance mai karfin zuciya tamkar Yarima Albert, wanda hakan ne ya sa ya kasa jurewa 'yan gargajiyar da koyaushe suke son a tsaya a kan gargajiya kuma suke zarginsa da daga kai.

Yarima Philip mutum ne wanda ya yarda da yin abu kai tsaye, hakan kuma ya bayyana a lokacin yake yake-yake, musamman ma lokacin da abokan gaba suka lalata jirgin yakinsu mai suna HMS Wallace a lokacin yana matsayin laftanal na soji.

Lokacin da hare-haren dare suka yawaita daga masu jefa bama-bamai na Luftwaffe, sai Philip ya kirkiri wata dabara, inda sukan samar da kiraren da ke fitar da hayaki, hakan yakan nuna kamar wurare suna ci da wuta, wannan ne ya dinga dauke hankalin masu sa bama-bamai, har dai wannan jirgin nasu na Wallace ya kubuta.

A lokacin da yake aikinsa na sojan ruwa, ya yi suna sosai a sakamakon burinsa na gyara gami da inganta abubuwa a koyaushe.

Sannan kuma ga shi ba ya dagawa 'yan ra'ayin gargajiya kafa, wannan ya sa wasu daga cikin abokan aikinsa ba sa son shi.

Bayan ya auri gimbiya Elizabeth a shekarar 1947 da kuma shigarsa gidan sarauta ya gano cewa abubuwa sun canja sabanin yadda suke tun zamanin sarauniya Bictoria.

Zakuwar da ya yi wajen ganin an dan sakarwa jama'a mara, ta sami fassara da dama, musamman ganin yadda mutanen fada suka karbe shi, musamma ma sakataren sarki George na 4 wato Tommy Lascelles, wanda Lord Brabourne ya bayyana da cewa, ya so ya haifar wa Yarima da matsala.

Na'urori suna ba shi sha'awa. Lokacin da suka tare a gidan Clarence a shekarar 1949 ya nishadantu sosai da saka na'urorin saukaka rayuwa wadanda suka hadar da wata na'urar fito da riga daga wajen ajiye kaya, da zarar an danna wani dan malatsi.

Sha'awarsa ga kimiyya da fasaha ce ta sa aka neme shi don ya zama shugaban kungiyar bunkasa kimiyya ta kasar Birtaniya.

Bayanan da ya yi a lokacin kaddamarwa, sun ba wa 'yan jarida sha'awa, inda kalaman nasa suka yi nuni ga Babban Baje-kolin fasahohi na 1851 na mutumin da ya gabace shi kuma kakan kakansa wato yarima Albert.

A wannan shekarar ne dai a bisa shawararsa, shi da gimbiya Elizabeth suka kai ziyarar aiki zuwa Canada.

Wannan ita ce ziyara ta farko da wani babban jami'i na gidan sarautar ya tsallaka kogin Atlantika, inda a wani salon a musamman, yariman ya zauna tare da matuka jirgin sama a yayin tafiyar yana tambayar su yadda ake tuka jirgin sama kirar BOAC.

Bayan dowowarsu, sai kuma ya koma kai ziyara zuwa masana'antu da cibiyoyin bincike da kuma tashoshin lantarki, inda manajojin wadannan wurare suka dinga shan tambayoyi daga bakon nasu.

Sha'awarsa game da cigaba, ta zo daidai da lokacin habakar aikace-aikacen fasaha a Birtaniya a shekarar 1950, inda a wadannan 'yan shekaru ne aka fara samun kwanfuyutocin zamani da kuma jiragen haya na farko na kamfani British Comet.

Irin wadannan lamura ne suka samar da rahotanni masu dadi daga 'yan jaridu, inda yarima ya ci gaba karfafar guiwar masana'antun Birtaniya da kuma ci gaba da farfadowa da murmurewa daga tasirin yaki.

Hakazalika, sai kuma Yarima ya fara nuna irin sha'awar da kawunsa Lord Mountbatten yake da ita game da abubuwan da suke yawo a sararin samaniya, inda ya dinga bibiyar mujallar "The Flying Saucer Rebiew" wadda ta mai da hankali a kan bibiyar yiwuwar bayyanar bakin halittu a duniya, har ma ya umarci wani ma'aikacinsa Skn Ldr Peter Horsley da ya ci gaba da bibiyar rahotanni game da bayyanar irin wadannan abubuwan da za a iya ganin gittawarsu a sararin samaniya.

Bayan mutuwar George na 4 a cikin watan Fabrairun 1952, sai sabuwar sarauniya da mijinta suka koma rukunin gine-ginen fadar Buckingham sakamakon matsi daga fadawa.

Yarima Philip da matarsa wadda a yanzu ta zama mai rike da sarauta, sun sami sukuni duk da cewa a yanzu ba shi ke jan ragamar gidansa ba, da kuma kasancewar da ya yi cikin laluben irin rawar da zai taka.

Har ila yau, irin tarbar ko-oho da aka yi masa a fadar ta ci gaba da sosa masa rai, inda ya fara zuzzurfan bincike dangane da yadda ake gudanar da harkokin fada.

Ya dinga kai wa da kawowa a tsakanin kimanin dakuna 600 inda yake tambayar kowane ma'aikaci game da irin rawar da yake takawa.

An sami raguwar adadin ma'aikata bayan yarima Philip ya gano cewa wasu manyan ma'akatan fada, aikin nasu kawai na je-ka-na-yi-ka ne, wasu kuma ba sa aikin komai sai dai barci a dakunansu.

Wasu daga cikin tsofaffin fadawa sun nuna rashin jin dadinsu game da tsoma bakin da yake, inda daga baya daya daga cikin tsofaffin ma'aikata kuma mataimakin jami'in samar da kayayyaki wato Frederick Corbitt ya yarda cewa yarima Philip yana yin tambayoyin da suka dade, su da kansu, suna neman amsarsu.

Ya saka tarho a sassan fadar domin saukaka wa bayi kai sakonni zuwa ga matarsa da ke can daya bangaren fadar.

Har ila yau, ya sami yabo daga sojojin kafa a bisa kokarinsa na kawo karshen dadaddiyar al'adar nan ta shafa shuni a gashinsu, wadda ta kai kusan shekara dari.

Yarima Philip ya sha karya tsarin al'adun fada, inda ya gwammace ya dauki kayansa da kansa maimakon ya danna kararrawa domin kiran fadawa 'yan aike, ko kuma ka gan shi yana dafa abincin karin kumallo a dakinsa har sai da sarauniya ta yi korafin kauri yana damunta.

Har ila yau, bayan ya gano cewa fadar tana da dakuna girki guda biyu, daya na sarakai, daya kuma na ya-ku-bayi, sai ya sa aka rufe daya.

Hakazalika ya kudiri aniyar zamanantar da sarautar baki dayanta.

Ya gano cewa akwai sauye-sauyen da suka faru a cikin al'ummar Birtaniya, wadanda suka haifar da samuwar sabon zamanin bayan yakin duniya wanda bai dace da tsarin da ake kai a da ba.

Yarima Philip na cikin na gaba-gaba wajen goyon bayan soke tsohuwar al'adar nan ta karbar 'yan mata a fada a 1958 wadda aka shafe sama shekaru 200 ana yi.

Har ila yau, ya kirkiro wata sabuwar al'adar taron cin abincin rana, inda sarauniya take samun damar ganawa da mutane daga sassa daban-daban na masarautarta.

A shekarar 1968 an shigo da BBC wadda ta dade tana kokarin samun hanyoyin sadar da masarautar ga jama'a.

Yarima Philp ya ci gaba da karfafar shirin, inda ya shugabanci kwamitin da aka kafa domin samar da dabaru tabbatar da shirin, haka kuma, sai ya dauki Richard Cawston domin samar da shirin fim domin hakan.

Sakamakon hakan aka samar da wani shirin fim na tarihi mai suna "Gidan Sarauta" mai tsawon minti 90, wanda aka nuna a shekarar 1969.

Wannan fim ya sami karbuwa sosai inda ya zama tamkar wani abu na tarihi ta yadda mutane suka fara ganin kwaikwayon yadda rayuwar gidan sarauta take tare da kuma jin irin hirarrakin da a da, na sirri ne.

An nuna wannan fim a ko'ina a fadin duniya, kuma shirin ya taimaka matuka wajen sauya tunani na sarautar gado zuwa tsarin gidan sarauta.

Ya kasance mai hangen nesa duk da kasancewar shekarunsa sun mika.

A shekarar 2015 ya shiga karkashin kasa domin duba aikin titin jirgin kasa mai dogon zango na London.

Bayan da aka bayyana masa cewa ana sa ran rukunin jiragen farko za su fara aiki ne a 2018, sai ya nuna cewa, zai yi wuya ya kai lokacin. Bayan ya dan yi shiru, can, sai ya kara da cewa "Amma dai da wuya in kai laokacin".

Dukkanin hotuna da hakkin mallakar Getty Images da Alamy da Rex Shutterstock da kuma Press Association ne.