You are here: HomeAfricaBBC2023 05 25Article 1773926

BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023

Source: BBC

Pirlo ya ajiye aikin horar da Fatih Karagumruk ta Turkiya

Andrea Pirlo Andrea Pirlo

Andrea Pirlo ya ajiye aikin horar da kungiyar kwallon kafa ta Turkiya, Fatih Karagumruk, yayin da ya rage saura wasa uku a kammala kakar bana.

Mai shekara 44 ya koma Istanbul a cikin watan Agusta, wanda ya yi fatan daga darajarsa a kungiyar, bayan da Juventus ta kore shi a 2021.

Kungiyar ta Turkiya ta sanar cewa mataimakin Pirlo, Alparslan Erdem, ya karbi aikin zuwa karshen kakar nan.

Pirlo, wanda ya karbi aikin yarjejeniyar kaka daya, ya lashe Champions Leagues biyu da Serie Ashida a lokacin da ya taka leda a AC Milan da Juventus.

Yana kuma cikin 'yan wasan da suka lashe wa Italiya kofin duniya a 2006.

An sanar da nada Pirlo kociyan Juventus a cikin watan Agustan 2020, wanda ya ja ragamar kungiyar Turin ta lashe Italian Cup.

Sai dai an kore shi a 2021, bayan da Juventus ta fice daga Champions League a zagayen 'yan 16 da yin ta hudu a teburin Serie A.

Hakan ne ya sa Juventus ta kasa daukar babban kofin tamaula na Italiya, bayan da ta ci tara a jere.

Kawo yanzu Karagumruk tana ta tara a teburin gasar Turkiya ta Super Lig, wadda saura karawa uku a kammala wasannin bana.