You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811906

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Pillars ta naɗa sabon koci

Yan wasan Kano Pillars | Hoton alama Yan wasan Kano Pillars | Hoton alama

An bayyana koci Abdullahi Maikaba a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Koci Abdullahi Maikaba ya rattaba hannu kan kwangilar shekara biyu da Sai Masu gida daga kakar wasan 2023/2024 zuwa 2024/2025.

Koci Maikaba zai samu taimakon Abubakar Abubakar wanda aka fi sani da Ahmad Garba Yaro Yaro da Gambo Muhammad da kuma Auwalu Abbas a matsayin mai horar da masu tsaron gida.

Da yake kaddamar da sabon babban mai kula da kungiyar a ofishinsa, mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu AbdulSalam Gwarzo, ya bukace shi da ya zage damtse domin farfado da martabar kungiyar.

Kwamared Aminu AbdulSalam Gwarzo ya taya shi murna tare da bayyana nadin nasa a matsayin wanda ya dace ganin irin dumbin kwarewarsa a harkar koyar da kwallon kafa a kungiyoyin kwallon kafa daban-daban na Najeriya.

Mataimakin Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da bai wa kungiyar goyon baya domin ganin an cimma burin da aka sanya a gaba sannan kuma ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar Kano za ta kara kaimi wajen gyaran filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata Kano.

Ya yaba wa shugabannin kungiyar da ‘yan wasan kungiyar bisa kwazon da suka nuna wanda ya sa kungiyar ta koma gasar Premier.

Da yake mayar da martani, Abdullahi Maikaba ya gode wa mahukuntan kungiyar da suka amince da shi sannan ya yi alkawarin tabbatar da amincewar da aka yi masa.