You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837739

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Palhinha na cikin rashin tabbas, Ramos na nazarin tafiya Sevilla

Joao Palhinha Joao Palhinha

Ɗan uwan Joao Palhinha ya shaida cewa ɗan wasan mai shekara 28 asalin Portugal da ke taka leda a Fulham, an ɗage batun komawarsa Bayern Munich, bayan gaza cimma jituwa har lokacin cikar wa'adi. (Mail)

Tsohon Kyeftin ɗin Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 37, na tattaunawa kan koma wa Sevilla, kungiyar da ya bari shekaru 18 da suka gabata zuwa Real Madrid. Ɗan wasan na baya ya bar Paris St-Germain a wannan kakar bayan cikar wa'adin kwantiraginsa. (ESPN)

Ƙungiyar Ligue 1 Lorient ta sake nazari kan ɗan wasan Netherlands mai buga tsakiya Donny van de Beek, mai shekara 26, saboda halayen da ya nuna lokacin da ya cimma yarjejeniyar tafiya zaman aro a Manchester United. (L'Equipe - in French)

Chelsea ta buɗe hanya ga Tottenham domin saye ɗan wasan Ingila mai buga tsakiya James Maddison, mai shekara 26, a karshen kaka saboda shekarunsu ba su yi daidai da bukantunsu ba.(Football Insider)

Tsohon ɗan wasan Manchester United kuma mai tsaron raga a Sifaniya David de Gea, mai shekara 32, na cikin 'yan wasan da kwantiraginsu ya kare, wanda kuma ke jan hankalin ƙungiyoyin Saudiyya. (Marca - in Spanish)

Ɗan wasan Atletico Madrid da Belgium Yannick Carrasco, mai shekara 29, na shirin komawa ƙungiyar Saudiyya ta Al Shabab a kan fan miliyan 12.8. (ESPN)

Koci Wayne Rooney na fatan sake sayen ɗan wasan Jamaica Ravel Morrison, mai shekara 30 da ɗan wasan Ingila Jesse Lingard shi ma mai shekara 30, da kuma mai buga gaba a Ghana Andre Ayew, mai shekara 33, wanda yanzu haka babu wata yarjejeniyar ƙungiya a kan su. (Washington Post - subscription required)

Kungiyar Monaco da ke buga Ligue 1 na shirin sayen ɗan wasan Fulham Tosin Adarabioyo, mai shekara 25, a watan Janairu bayan matsawa ta saye shi a karshen kaka.(Fabrizio Romano)

Barcelona ta nuna rashin jindadinta da Manchester City saboda kokarin saye ɗan wasan Sifaniya Alejandro Balde, mai shekara 19, da mai buga gefe Lamine Yamal mai shekara 16 da kuma matashin ɗan wasan Sifaniya Pau Cubarsi, mai shekara 16, a wannan kakar. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Ɗan wasan Chelsea da Brazil Thiago Silva, mai shekara 38, ya yi sa-in-sa da magoya baya a Instagram bayan lalasa kungiyar ta Firimiya a fafatawarsu da Nottingham Forest a ranar Asabar. (Telegraph - subscription required)