You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798547

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

PSG ta ɗauki Luis Enrique a matsayin sabon kocinta

Luis Enrique (tsakiya) tare da yan wasan Barcelona Luis Enrique (tsakiya) tare da yan wasan Barcelona

PSG ta ɗauki tsohon kocin Barcelona da Spaniya Luis Enrique a matsayin sabon kocinta.

Dan asalin ƙasar Sifaniya mai shekara 53 ya maye gurbin Chistophe Galtier ne, wanda aka kora bayan ya lashe Lig 1 a kakarsa ta farko.

Luis Enrique ya sanya hannu ne kan kwantaragin shekara biyu da ƙungiyar ta Faransa.

Wannan ne aiki na farko da ya samu tun bayan ajiye aikin ƙasarsa Sifaniya da ya yi a watan Disamba bayan Morocco ta fitar da su daga gasar a zagayen 'yan 16 a bugun fenariti a gasar cin Kofin Duniya na 2022.

Amma aikinsa na ƙarshe a ƙungiya shi ne a Barcelona, inda ya lashe kofuna tara a kaka uku da ya yi tsakanin 2014 zuwa 2017, ciki har da Champions da La Liga da Copa del Rey, ya ci kofi uku a shekara guda.

A 2018, ya maye gurbin Fernando Hierro wanda ya kai ƙasar wasan ƙarshe a gasar National League da kuma wasan kusa da na ƙarshe a gasar zakarun nahiyar Turai a 2021, kafin ya jiye aiki bayan dawowarsu daga Qatar.

Gabanin ya zo ƙungiyar Galtier ya maye gurbin Mauricio Pochettino a bara.