You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816580

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

Source: BBC

PSG na zawarcin Dembele

Ousmane Dembele Ousmane Dembele

Akwai alamun cewa Ousmane Dembele zai iya barin Barcelona a wannan bazara, inda aka samu rahoton cewa Paris St-Germain na sha'awar sayen ɗan wasan.

Fabrizio Romano ya ruwaito cewa tuni Bafaranshen ya amince da yarjejeniyar shekara biyar da zakarun Gasar Ligue 1 .

Ɗan wasan mai shekara 26 yana da kuɗin tafiya na Yuro miliyan 50 (£43m) a kwantiraginsa da Barca - wanda ya ƙare a ranar 1 ga watan Agusta. Babu tabbas a kan ko PSG ta miƙa tayi a cikin wannan wa'adin.

An kuma samu labarin cewa kocin Barca, Xavi ya shiga tsakani domin ya shawo kan Dembele ya ci gaba da zama a kulob ɗin.

Yanzu za a fara tattaunawa.

Barcelona ta ba shi kwana biyar ya zo da tayi daga PSG.

A halin yanzu, Barcelona ba ta karɓi tayi daga PSG a kan ɗan wasan ba.